Don Allah kada ku bar makiyaya suyi kiwo a jiharmu - Ortom ga Sarakunansa

Don Allah kada ku bar makiyaya suyi kiwo a jiharmu - Ortom ga Sarakunansa

- Jihar Benue ta cika shekara da kisan 73

- Makiyaya ne ke kashe kauyawa manoma

- Wannan yasa jihar ma ta koma PDP

Don Allah kada ku bar makiyaya suyi kiwo a jiharmu - Ortom ga Sarakunansa

Don Allah kada ku bar makiyaya suyi kiwo a jiharmu - Ortom ga Sarakunansa
Source: Twitter

A lokacin da ake dab da shiga zabukan gwamnoni da shugaban kasa, jihar Binuwai na kara fayyace ra'ayinta na siyasa na kin jinin arewa da jama'arta.

Wannan na zuwa ne a lokacin da jihar ke bikin cika shekara guda da kashe mutum 73 a watan Yanairun bara, wanda fulani makiyaya suka yi.

A wancan lokaci dai, makiyayan sun kashe mata, maza, yara da ma matasa suka kone musu kauyukansu.

DUBA WANNAN: Katobara! An jiyo Amaechi na caccakar Buhari, bai so hakan ta fallasa ba

Gwamna Ortom, yayi kira ga Sarakunansa, da suyi wa Allah da dansa Yesu, su hana makiyaya rangadi a yankunansu da shanunsu, su kore su ko su gaya wa hukuma.

Dama dai anyi dokar hana kiwo a jihar, duk wasu dabbobi da aka kama gwamnati tana kwace su, tare da gurfanar da masu karya dokar.

Miyetti Allah dai kance su masu zaman lafiya ne, amma ana sace musu shanu a kai Legas a sayar, ko a cinye.

Dama a makon jiya makiyayan suka babbake wa gwamnan gonarsa ta shinkafa, wadda ta bushe qaraf sai girbi, ya tafka asarar N100m.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel