Kwamishinoni 6 na gwamnan APC sunyi murabus

Kwamishinoni 6 na gwamnan APC sunyi murabus

A yau Litinin 7 ga watan Janairun 2019 ne kwamishinoni guda shida a jihar Ogun su kayi murabus daga mukamansu a gwamnatin Gwamna Ibikunle Amosun.

Kwamishinonin sun hada da Mrs Ronke Sokefun (Kwashinan Tsare-tsaren birane); Mrs Adepeju Adebajo (Ma'aikatan Noma); Leke Adewolu (Ayyuka na musamman); Adedayo Adeneye (Yadda labarai da tsare-tsare); Kolawole Lawal (Gandun Daji) and Modupe Mujota (Ilimi, kimiyya fa fasaha).

Daily Trust ta ruwaito cewa Sokefun tayi murabus ne domin ta fara aiki a matsayin Ciyaman din Kwamitin (NDIC), sauran kwamishinoni 6 kuma sunyi murabus ne domin su samu damar tsayawa takarar kujerun siyasa a babban zaben 2019.

Kwamishinoni 6 na gwamnan APC sunyi murabus

Kwamishinoni 6 na gwamnan APC sunyi murabus
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Sunaye: Manyan jaruman Kannywood dake cikin kwamitin kamfen din Aisha

Wani hadimin gwamnan, Direkta Janar na Ma'aikatan Filaye, Biyi Ismail ya ajiye mukaminsa domin takarar a babban zaben da za a yi a watan Fabrairun shekerar 2019.

A jawabinsa da ya yi a wajen taron bankwana da hadimansa da akayi a ofishin gwaman da ke Oke-Mosan a Abeokuta, Amosun ya mika godiyarsa da hadiman nasa saboda ayyukan da suka yiwa jihar da goyon bayan gwamnatinsa.

Ya ce,"rawar da suka taka a yayin gudanar da ayyukansu ya taimaka gaya wajen cimma burinsa na 'sake gina jihar Ogun' kuma ya musu fatan alheri a dukkan abinda suka sanya a gaba."

Tsaffin kwamishinonin suma sun mika godiyarsu ga gwamnan inda suka gode masa bisa damar da ya basu na yiwa jiharsu hidima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel