Mika wuka da nama a hannun Tinubu ba hujja bace na kin halartan muhawarar shugaban kasa – Atiku ga Buhari

Mika wuka da nama a hannun Tinubu ba hujja bace na kin halartan muhawarar shugaban kasa – Atiku ga Buhari

- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci shugaban kasa Buhari da ya kwana da sanin cewa Tinubu ba zai iya wakiltan shi a muhawarar yan takarar shugaban kasa

- Hakan martani ne ga cewa da Buhari yayi ya bar wuka da nama na kamfen dinsa a hannun Tiubu

- Kungiyar muhawarar zabe ta shirya wa yan takarar shugaban kasa Muhawara a ranar 19 ga watan Janairun, 2019

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya yi tunanin mika karagar kamfen din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ga jigon jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, zai zama hujjar da zai sa yaki halartan muhawaran yan takarar shugaban kasa.

Kungyar muhawarar zabe ta shirya wa yan takarar shugaban kasa Muhawara a ranar 19 ga watan Janairun, 2019.

Mika wuka da nama a hannun Tinubu ba hujja bace na kin halartan muhawarar shugaban kasa – Atiku ga Buhari

Mika wuka da nama a hannun Tinubu ba hujja bace na kin halartan muhawarar shugaban kasa – Atiku ga Buhari
Source: Facebook

Kakakin kungiyar kamfen din Atiku, Segun Soowunmu a wani hira ya bayyana cewa abun bakin ciki ne sauranyan takarar shugaban kasa sun mayar da hankali suna kamfen kuma suna shirin amsa tambayoyin mutane, amma sai gashi shugaba Buhari na kaurace ma kamfen saboda bashi da abun yin kamfen din.

Sowunmi yace hakan ya kuma nuna cewa shugaban kasar bai da abunda ake bukata wajen yin kamfen da shugabancin kasar.

KU KARTA KUMA: Damuwa ya cika PDP yayinda shugaban jam’iyyar da wasu fusatattun yan takara suka koma APC

A wani lamari na daban, mun ji cewa akalla mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 2,800 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a yankin Madobi da Daura da ke jihar Katsina.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa masu sauya shekar sun samu tarba a kauyen Madobi daga shugaban APC na karamar hukumar Daura, Alhaji Sani Altine-Daura a ranar Litinin, 7 ga watan Janairu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel