Ba bu dalibin mu da aka kashe ko aka yi garkuwa da shi - Jami'ar Al-Qalam

Ba bu dalibin mu da aka kashe ko aka yi garkuwa da shi - Jami'ar Al-Qalam

- An yi rade-radin garkuwa da wasu dalibai na jami'ar Al-Qalam

- Hukumar Jami'ar da ke jihar Katsina ta ce ba bu dalibinta ko guda da aka samu rahoton garkuwa ko kisan sa

- Hukumar 'yan sandan jihar Katsina ta ce zance ne na shaci fadi da kanzon kurege

Jami'ar Al-Qalam ta jihar Katsina ta karyata rade-radin da ke yawo a zaurukan sada zumunta na garkuwa tare da kashe wasu daliban ta. Ta ce ba bu dalibinta ko guda da aka samu rahoton batansa, garkuwa ko kisa daga bangaren jami'an tsaro ko iyaye.

Cikin wani jawabi da ya fito daga sashen kula da walwala da kuma hulda da al'umma na jam'iar ya bayyana cewa, an tuntubi sahihancin wannan lamari daga kafofin tsaro daban-daban da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki.

Ba bu dalibin mu da aka kashe ko aka yi garkuwa da shi - Jami'ar Al-Qalam

Ba bu dalibin mu da aka kashe ko aka yi garkuwa da shi - Jami'ar Al-Qalam
Source: UGC

A yayin da hakan ake bukata hakar kuwa ba ta cimma ruwa ba sakamakon rashin bayyanar wani rahoto da zai tabbatar da afkuwar wannan lamari ko kuma mai kama da hakan kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta bayyana.

Rade-radin da ke yawo na nuni da cewa, anyi garkuwa da wasu dalibai kimanin su 9 na jami'ar Al-Qalam akan hanyar su ta Kankara zuwa Dutsinma a jihar Katsina.

KARANTA KUMA: Zan bar gadon tsarkakken zabe na adalci a Najeriya - Buhari

Wata majiyar rahoton maras tushe ta bayyana cewa, tuni masu hannu cikin wannan muguwar ta'ada sun kashe dalibai hudu yayin da suke ci gaba da garkuwa da sauran har sai an biya kudin fansar su na Naira miliyan ashirin.

Yayin tuntubar kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, SP Gambo Isah ya bayyana cewa, wannan wani rahoto ne na shaci fadi da kuma kanzon kurege maras tushe ko madogara da za ta tabbatar da sahihancinsa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel