Buhari ya nada Modibbo Tukur a matsayin daraktan sashin kwararru na kudin Najeriya

Buhari ya nada Modibbo Tukur a matsayin daraktan sashin kwararru na kudin Najeriya

- Shugaban Buhari ya nada Modibbo Hamman Tukur a matsayi darkta na sashin kwararru na kudin Najeriya wato Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU)

- Kakakin shugaban kasa Femi Adesina ne ya sanar da hakan

- Tukur dan asalin jihar Adamawa ya mallaki digiri na biyu a fannin kasuwancin kasa da kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a nada Modibbo Hamman Tukur a matsayi darkta na sashin kwararru na kudin Najeriya wato Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU).

Mista Femi Adesina, kakakin shugaban kasa wanda ya bayyana hakan a wani jawabi da ya sani a Abuja a ranar Litinin, 7 ga watan Jairu yace nadin yayi daidai sa sashi 5(1) na dokar hukumar Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU) 2018.

Buhari ya nada Modibbo Tukur a matsayin daraktan sashin kwararru na kudin Najeriya

Buhari ya nada Modibbo Tukur a matsayin daraktan sashin kwararru na kudin Najeriya
Source: Twitter

“Hakan na kunshe a wani wasika mai kwanan wata 7 ga watan Janairu, 2019 zuwa ga shugaban majalisar dattaa inda aka nemi a tabbatar da shi” cewar shi.

Tukur dan asalin jihar Adamawa ya mallaki digiri na biyu a fannin kasuwancin kasa da kasa.

A yanzu haka ya kasance mataimakin darakta a NFIU, sannan yana da kwarewa a fannin dawo da kadarorin da aka mallaka a waje ba bisa ka’ida ba.

KU KARANTA KUMA: Babu wani bayani daga fadar shugaban kasa kan ritayan IGP Ibrahim Idris – Hukumar yan sanda

Hukumar NFIU wani sashi ne a hukuar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) da ke aiki a nahiyar Afrika

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel