2019: Tinubu ba zai bawa Buhari kunya ba - Kungiya

2019: Tinubu ba zai bawa Buhari kunya ba - Kungiya

Kungiyar yakin neman zaben Buhari (BCO) ta goyi bayan nadin jagoran jam'iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaba na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa.

Ta ce tsohon gwamnan jihar Legas din ba zai bawa jam'iyyar APC da Shugaba Buhari kunya ba duba da irin gogewarsa da kwarewa a siyasa.

Kungiyar ta fitar da wannan sanarwan ne bayan wasu kafafen watsa labarai sun fitar da wani rahoto da ke cewa an samu rashin jituwa a jam'iyyar na APC bayan shugaba Muhammadu Buhari ya zabi 'yan kwamitin yakin neman zabensa.

Rahoton ya ce wasu gwamnonin jihohi da jiga-jigan jam'iyyar na APC ba su gwamsu da kwamitin ba saboda wai galibin 'yan kwamitin magoya bayan Bola Tinubu ne.

2019: Tinubu ba zai bawa Buhari kunya ba - Kungiya

2019: Tinubu ba zai bawa Buhari kunya ba - Kungiya
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Fallasa : Dan Boko Haram ya tona asirin yadda suke kai harin bam din Nyanya

Sai dai a sanarwar da kungiyar ta fitar da bakin direktan sadarwa da tsare-tsaren ta, Mallam Gidado Ibrahim, ta ce babu wani abin damuya a jam'iyyar.

Ta kara da cewa idan ma akwai wani rashin jituwa a tsakanin jam'iyyar, ba wani abin damuwa bane domin hakan dama yana iya faruwa.

Kungiyar ta ce babu wanda yafi dacewa da jagorancin yankin zaben shugaban kasar baya ga Tinubu musamman a wannan lokacin da jam'iyyar ke fuskantar babban zabe daf da sulhun da akayi tsakanin 'yan jam'iyyar.

Ibrahim ya ce, "Idan ana la'akari da shugabanci ne a jam'iyya, Tinubu shine wadda ya fi dacewa da shugabancin.

"Nada shi shugaban kwamitin sulhu na jam'iyya ya biya bukata. Munyi imanin wannan kamar yadda ya jagorancin APC har aka samu nasara a 2015, hakan ma zai sake faruwa yanzu da aka nada shi a matsayin shuagan yakin neman zabe.

"Wadanda suke damuwa da rahotannin da ake yadawa su kwantar da hankalinsu su bawa Tinubu hadin kai domin samun nasara a babban zaben 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel