Mambobin PDP 2,800 sun sauya sheka zuwa APC a mahaifar Buhari

Mambobin PDP 2,800 sun sauya sheka zuwa APC a mahaifar Buhari

- Akalla mambobin jam’iyyar PDP 2,800 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a yankin Madobi da Daura da ke jihar Katsina

- Masu sauya shekar sun samu tarba a kauyen Madobi daga shugaban APC na karamar hukumar Daura, Alhaji Sani Altine-Daura a ranar Litinin, 7 ga watan Janairu

- Sani ya basu tabbacin cewa za a kula da su kamar sauran yan jam’iyya sannan yayi alkawarin tafya tare da kowa wajen gudanar da ayyukan jam’iyyar ba tare da nuna wariya ba

Rahotanni sun kawo cewa akalla mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 2,800 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a yankin Madobi da Daura da ke jihar Katsina.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa masu sauya shekar sun samu tarba a kauyen Madobi daga shugaban APC na karamar hukumar Daura, Alhaji Sani Altine-Daura a ranar Litinin, 7 ga watan Janairu.

Mambobin PDP 2,800 sun sauya sheka zuwa APC a mahaifar Buhari

Mambobin PDP 2,800 sun sauya sheka zuwa APC a mahaifar Buhari
Source: Depositphotos

Shugaban ya basu tabbacin cewa za a kula da su kamar sauran yan jam’iyya sannan yayi alkawarin tafya tare da kowa wajen gudanar da ayyukan jam’iyyar ba tare da nuna wariya ba

Malam Iliyasu Shehu, tsohon shugaban karamar hukumar, wanda yayi Magana a madadin masu sauya shekar ya bayyana cewa sun yake shawarar ne domin kawo ci gaba yayinda zabe ke dada gabatowa.

KU KARANTA KUMA: Babu wani bayani daga fadar shugaban kasa kan ritayan IGP Ibrahim Idris – Hukumar yan sanda

Ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar ne ba tare da wani ka’ida ba cewa jam’iyyar APC karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta yi kokari matuka muusamman wajen samar da kayayyakin more rayuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel