Boko Haram: Kashim Shettima ya jagoranci dattijan jihar Borno zuwa wurin Buhari, hotuna

Boko Haram: Kashim Shettima ya jagoranci dattijan jihar Borno zuwa wurin Buhari, hotuna

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya saka kuka a gaban shugaba Buhari a kan koma bayan da ake samu a bangaren yaki da Boko Haram a jihar sa.

Hakan ya faru ne yau, Litinin, a Abuja yayin da gwamnan ya gana da Buhari a fadar sa tare da rakiyar wasu shugabannin hukumomin tsaro.

Shettima ya jagoranci shugabanni daga jihar Borno domin ganawa da Buhari domin tattauna matsalolin tsaro a jihar Borno.

"A tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014, mun fuskanci tsananin hare-hare daga kungiyar Boko Haram da ta kai ga sun kwace iko da kananan hukumomi 20," a cewar Shettima.

Boko Haram: Kashim Shettima ya jagoranci dattijan jihar Borno zuwa wurin Buhari, hotuna

Kashim Shettima ya jagoranci dattijan jihar Borno zuwa wurin Buhari
Source: Twitter

Sannan ya cigaba da cewa, "mun garzayo wurinka ne saboda koma bayan da ake samu yanzu haka a yaki da Boko Haram. Mun zo wurinka ne saboda irin kokarin da ka nuna a kan matsalar tsaro a jihar mu tun bayan hawanka mulki a shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Sunaye: Manyan jaruman Kannywood dake cikin kwamitin kamfen din Aisha

"Mai girma shugaban kasa, bamu fitar da ran cewar zaka cece mu daga halin da muke ciki ba. Bamu daina kyautata maka zato ba, kuma mun san zaka iya.

"Mun zo nan ne da wasu bukatu guda goma da kuma shawarwari da muke son tattaunawa da kai. Hakan ya biyo bayan wata tattaunawa mai tsayi da muka yi a taron kwamitin tsaro na jihar Borno a cikin satin da ya gabata.

"Mun dauki lokaci bayan taron kafin daga bisani mu yanke shawarar zuwa mu gana da kai. Mun ziyarci gabashin jihar Borno domin ganawa da mazauna sansanin 'yan gudun hijira da kuma kara wa dakarun soji karfin gwuiwa.

"Ina son manema labarai su yi min afuwa don bukatu 10 da muke da su na sirri ne, ba zan iya fada a gabansu ba saboda dalilan tsaro."

Fashewar gwamnan da kuka ya sa an umarci manema labarai ficewar daga wurin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel