Damuwa ya cika PDP yayinda shugaban jam’iyyar da wasu fusatattun yan takara suka koma APC

Damuwa ya cika PDP yayinda shugaban jam’iyyar da wasu fusatattun yan takara suka koma APC

- Jam’iyyar PDP na cikin damuwa kan sauya shekar tsohon shugabanta na jihar Niger, Abdulrahman Enagi, wata daya gabannin zaben kasa baki daya

- Enagi ya sauya shekane tare da tsoffin yan takarar kujerar gwamna su biyu Ahmed Baka da Engineer Hanafi Sudan, da kuma wasu inda suka koma jam’iyyar APC

- PDP ta bayyana wadanda suka sauya shekar a matsayin bara-gurbi a jam’iyyar

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cikin damuwa kan sauya shekar tsohon shugabanta na jihar Niger, Abdulrahman Enagi, wata daya gabannin zaben kasa baki daya.1

NAN ta ruwaito cewa Enagi ya sauya sheka ne tare da tsoffin yan takarar kujerar gwamna su biyu Ahmed Baka da Engineer Hanafi Sudan, da kuma wasu inda suka koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Damuwa ya cika PDP yayinda shugaban jam’iyyar da wasu fusatattun yan takara suka koma APC

Damuwa ya cika PDP yayinda shugaban jam’iyyar da wasu fusatattun yan takara suka koma APC
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa PDP ta bukaci magoya bayan jam’iyyar da su zamo masu alkibla sannan kada su bari yunkurin wasu yan tsirarun mutane ya ja hankalinsu.

Ta bayyana wadanda suka sauya shekar a matsayin bara-gurbi a jam’iyyar, Tanko Beji, shugaban PDP na jihar ya bayyana cewa jam’iyyar bata damu da yawan sauye-sauyen shekar da aka samu a makon da ya gabata ba inda ya kara da cewa masu sauya shekar ba komai bane.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago za ta gudanar da zanga-zanagar gama gari a gobe Talata

Enagi, Baka, Sudan da kuma ma’ajin PDP a jiharm Ibrahim Ibeto da wani dan takarar shugaban kasa a kungiyar wasa na Najeriya kuma tsohon ministan wasanni, Alhaji Sani Ndanusa sun bar jam’iyyar a kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel