2019: Atiku zai inganta ilmi a Najeriya muddin ya samu mulki – Jenifer Atiku

2019: Atiku zai inganta ilmi a Najeriya muddin ya samu mulki – Jenifer Atiku

Jeniffer Atiku wanda tana cikin iyalin ‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP, Alhaji Abubakar Atiku, ta bayyana cewa idan har ‘Dan takaran na jam’iyyar PDP yayi nasara a zaben bana, za a ga cigaba a harkar ilmi.

2019: Atiku zai inganta ilmi a Najeriya muddin ya samu mulki – Jenifer Atiku

Jenifer Atiku tace gwamnatin Atiku zai inganta harkar ilmi
Source: Twitter

Misis Jennifer Atiku, tayi wannan jawabi ne lokacin da aka kaddamar da takarar kujerar wani ‘dan majalisa a jihar Edo a makon da ya gabata. Misis Atiku tace idan mai gidan na ta ya samu mulki, za a ga karshen yajin aiki a makarantu.

Mai dakin ‘dan takarar shugaban kasar ta ke cewa idan PDP ta kafa gwamnati, za a daina zaman banza saboda yajin aikin da malaman jami’o’i su ke yi. Jennifer ta kuma ce gwamnatin PDP za ta tallafawa ‘yan kasuwa domin rage talauci.

KU KARANTA: Abokin takarar Atiku ya karyata cewa wasu manyan PDP su na shirya masu zagon-kasa

Yanzu haka kungiyar ASUU ta malaman jami’o’in gwamnati sun yi watanni 2 su na yajin aiki babu kakkautawa. Matar tsohon mataimakin shugaban kasar tace akwai bukatar a gyara Najeriya domin jama’a su ji dadin zama a kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari, manyan PDP da su ka halarci wannan taro sun yabawa goyon bayan da mutanen yankin Edo ta tsakiya su ke ba jam’iyyar PDP tun dawowar mulkin farar hula a 1999.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel