Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace wani basarake a jihar Katsina

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace wani basarake a jihar Katsina

Mun samu rahotin cewa 'yan bindiga sun sace dagacin kauyen Zandam da ke karamar hukumar Jibia na Jihar Katsina, Babangida Lawal a daren jiya.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun sace basaraken ne tare da wani 'yan kasuwa a kauyen, Muratala Rabe a cewar wasu mazauna kauyen.

Majiyar Legit.ng ta ce 'yan bindiga sun iso kauyen cikin dare ne inda suka nufi gidajen mutanen biyu kuma su kayi awon gaba da su.

Wasu mazauna kauyen sunyi kokarin ceto su amma ba suyi nasara ba sai dai sun sami munanan raunuka.

'Yan bindiga sunyi awon gaba da wani basarake a jihar Katsina

'Yan bindiga sunyi awon gaba da wani basarake a jihar Katsina
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Fallasa : Dan Boko Haram ya tona asirin yadda suke kai harin bam din Nyanya

Kawo yanzu, 'yan bindigan basu nemi a biyu su kudin fansa ba domin su sako su.

An kuma gano cewa 'yan bindigan sun sace shanu masu yawa a kauyen Gurbi Magarya da ke makwabtaka da Zandam.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jiha, SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce "'yan sanda suna kokarin ceto wadanda ake sace".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel