Gwamnan jihar Borno ya fashe da hawaye yayin ganawa da Buhari kan rikicin Boko Haram

Gwamnan jihar Borno ya fashe da hawaye yayin ganawa da Buhari kan rikicin Boko Haram

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya tsinke da hawaye yayin da ya jagoranci tawagar dattawan jihar sa domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, ya fashe da hawaye da tsakar ranar yau ta Litinin yayin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa ta Villa kan ta'azzarar ta'addancin kungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Gwamna Kashim a yau Litinin ya jagoranci tawagar dattawan jihar sa zuwa fadar shugaban kasa domin tattaunawa da shugaba Buhari dangane da tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram da ya sake kunno kai a Arewa maso Gabashin kasar nan.

Gwamnan jihar Borno ya fashe da hawaye yayin ganawa da Buhari kan rikicin Boko Haram

Gwamnan jihar Borno ya fashe da hawaye yayin ganawa da Buhari kan rikicin Boko Haram
Source: Depositphotos

Manema labarai sun ruwaito cewa, Shettima wanda tawagar sa ta iso fadar shugaban kasa da misalin karfe 2.30 na ranar yau cikin gaggawa ya dirfafi babban dakin taro na council chamber domin ganawa da shugaban kasa.

Wannan taro na gaggawa ya gudana ne biyo bayan makamanciyar ganawar da ta gudana cikin birnin Maiduguri a makon da ya gabata dangane da harkokin tsaro sakamakon sake kunno kai na ta'addancin Boko Haram musamman a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar nan.

KARANTA KUMA: 'Yan Sumoga sun salwantar da rayuwar jami'in Kwastam 1, sun raunata 1 a jihar Ogun

Cikin wadanda suka halarci taron sun hadar da Sanatoci uku masu wakilcin jihar a majalisar dattawa, 'yan majalisar wakilai na jihar, dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Sarakunan gargajiya da kuma shugabannin addinai.

Sauran mahalarta taron sun hadar da shugaban dakarun tsaro na Najeriya, babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, shugaban hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS, da kuma shugaban hukumar leken asiri ta NIA.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel