Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago za ta gudanar da zanga-zanagar gama gari a gobe Talata

Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago za ta gudanar da zanga-zanagar gama gari a gobe Talata

- Kungiyar kwadago na Najeriya za ta gudanar dazanga-zangar gama gari a anar Talata, 8 ga wata Janairu

- Za ta yi hakan ne domin karfafa bukatara na sake duba lamarin mafi karancn albashi daga N18,000 zuwa N30,000

- Babban sakataren kungiyar NLC a wani jawabi da ya saki yace babu batun zuwa yajin aiki a yanzu

Kungiyar kwadago na Najeriya ta ce za ta gudanar da zanga-zangar gama ari a anar Talata, 8 ga wata Janairu domin karfafa bukatara na sake duba lamarin mafi karancn albashi daga N18,000 zuwa N30,000.

Babban sakataren kungiyar NLC, Dr. Peter Ozo-Eson, a wani jawabi da ya saki yace babu batun zuwa yajin aiki a yanzu.

Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago za ta gudanar da zanga-zanagar gama gari a gobe Talata

Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago za ta gudanar da zanga-zanagar gama gari a gobe Talata
Source: Depositphotos

Ozo-Eson ya kuma bukaci mambobin jama’a da su yi watsi da batun cewa yajin aiki zai fara a gobe.

Ga yadda jawabin ya zo: “An janyo hankalinmu kan cewa wasu sashin labarai sun chanja matakin da muke shirin dauka domin martani kan jinkirin da aka samu wajen mika da aiwatar da karin albashi mafi karanci ga majalisar dokokin kasar wanda Shugaba Buhari bai yi ba.

“A tuna cewa kungyar kwadago ta kasa ta gana a ranar 17 ga watan Disamban shekarar da ya gabata sannan ta yi umurnin cewa mu yi zanga-zangar ma’aikata n agama gari idan har ba’a tura wa majalisar dokoki mafi karancin albashi ba a ranar 31 ga watan Disamba domin aiwatar das hi ba.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da Gabon

“Don haka mun sanar da cewa a ranar Talata, 8 ga watan Janairu 2019, akwai zanga-zangar gama gari a fadin jihohin Najerya duka. Hakan ba yana nufin yajin aiki bane."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel