Babu wani bayani daga fadar shugaban kasa kan ritayan IGP Ibrahim Idris – Hukumar yan sanda

Babu wani bayani daga fadar shugaban kasa kan ritayan IGP Ibrahim Idris – Hukumar yan sanda

- An shiga halin rashin tabbass a hukumar yan sandan Najeriya

- Hakan ya biyo bayan shirun da fadar shugaban kasa ta yi akan Sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris da ake sa ran yiwa ritaya bayan ya kammala shekaru 35 yana yiwa kasa hidima

- A ranar Alhamis, ga watan Disamba, 2018 dai ya cika shekaru 35 da fara aiki sannan kuma zai cika shekaru 60 a ranar 15 ga watan Janairu

An shiga halin rashin tabbass a hukumar yan sanda, bayan shirun da fadar shugaban kasa ta yi akan Sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris da ake sa ran yiwa ritaya bayan ya kammala shekaru 35 yana yiwa kasa hidima a ranar Alhamis, 3 ga watan Disamba, 2018.

Don haka, wata majiya a hukumar ta bayyana wa jaridar Vanguard cewa hukumar yan sandan na jira don ganin kowani hukunci gwamnatin tarayya za ta yanke akan IGP Ibrahim wanda zai cika shekara 60 a ranar 15 ga watan Janairn 2019.

Babu wani bayani daga fadar shugaban kasa kan ritayan IGP Ibrahim Idris – Hukumar yan sanda

Babu wani bayani daga fadar shugaban kasa kan ritayan IGP Ibrahim Idris – Hukumar yan sanda
Source: UGC

Bisa ga tsarin daukar ma’aikata, ya kamata wanda ke rike da kambun ofishin Sufeto Janar na yan sanda yayi murabus bayan ya shafe shekar 35 a aiki ko kuma ya cika shkaru 60, cikin biyun wanda ya fara zuwa ake la’akari da shi.

KU KARANTA KUMA: Yadda sojoji suka yi mana duka suka kuma kwace wayoyinmu kan zargin sata – Matasa

Wata majiya a hukumar, tace babu abunda hukmar yan sandan za ta iya yi kan gashin kanta, inda ya bayana cewa har yanzu kofa a bude take ga sufeton yan sandan wanda za cika shekara 60 a ranar 15 ga watan Janairu domin ya fara shiri kan ritayarsam sai dai idan shugaban kasa yana ganin akasin haka.

Ayyukan baya-bayan nan da sufeto janar na yan sandan yayi kamar sauya kwamishinonin yan sanda a jihohi bawai, da suka hada da Bauchi, Kogi, Imo, Edo, Bayelsa, Delta, Abia, da Akwa Ibom da sauransu bai nuna alamu na IGP da ya cikashekaru 35 akan aiki ba kuma wanda ke son yin ritaya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel