Innalillahi wa inna Ilaihi rajiun: Gobara ta halaka kananan yara 2 a Kano

Innalillahi wa inna Ilaihi rajiun: Gobara ta halaka kananan yara 2 a Kano

Wasu kananan yara guda biyu sun gamu da ajalinsu a daren Litinin, 7 ga watan Janairu a sanadiyyar wata gobara da tashi a gidansu dake unguwar Sharada Ja’en Yamma a cikin birnin Kano, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin hukumar kashe gobara ta jahar Kano, Alhaji Sa’idu Muhammad ya sanar da haka a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labaru, inda yace yaran da suka mutu sun hada da dan shekara 7 da dan shekara hudu.

KU KARANTA: Yan kasuwa sun tafka mummunan asara a wata gobara da ta tashi a kasuwan Kaduna

“Da misalin karfe 2:09 na tsakar dare ne wani mutumi mai suna Malam Bello Tukur ya kiramu ta wayar tarho yana shaida mana cewa gobara ta tashi a wani gida, samun wannan labara keda wuya muka garzaya gidan tare da motar kasha wuta da misalin karfe 2:15, inda muka kashe wutar.” Inji shi.

Sai dai Mohammed yace koda suka isa gidan basu tarar da iyayen yaran a gida ba, sun fita waje suna neman taimakon mutane domin a kashe wutar kuma a ceto musu yaransu da wutar ta rutsa dasu a cikin gidan.

Amma duk kokarin da aka yi na ceto yaran da ransu, hakan ya ci tura, sai dai jami’an hukumar sun dauko gawarwakin yaran, inda suka mikasu ga jami’an rundunar Yansanda bayan sun kashe wutar.

Daga karshe kaakaki Saidu yace zasu kaddamar da bincike don gano tabbataccen abinda ya janyo gobarar don kiyaye gaba, sa’annan yayi kira ga iyaye dasu yi taka tsantsan wajen amfani da duk wani abu da ka iya janyo gobara a gidajensu.

A wani labarin kuma, Yan kasuwa dake da shaguna a babbar kasuwar garin Kafanchan sun tafka mummunar asara bayan da wata gobara ta tashi a daren Litinin, 31 ga watan Disambar shekarar 2018, cikin karamar hukumar Jama’a ta jahar Kaduna.

Shaguna guda goma sha hudu ne suka kone kurmus, wanda ya janyo asarar naira miliyan daya da dubu dari biyar (N1,500,000), kamar yadda shugaban yan kasuwar, Alhaji Salisu Idris ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel