Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da Gabon

Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da Gabon

Gabon kasar da sojoji suka yi yunkurin yiwa juyin mulki a safiyar ranar Litinin, 7 ga watan Janairu ya kasance daya daga cikin manyan kasashen Afrika mai cike da albarkatun man fetur sannan kuma sama da shekaru 50 ahlin Bongo ke mulki a kasar.

Shugaban kasa mai ci a yanzu Ali Bongo, wanda ya gaji mulki daga mahaifinsa a shekarar 2009, baya nan tun a watan Oktoba bayan ya samu cutar shanyewar barin jikia kasar Saudiyya.

Ga wasu daga cikin bayanin kasar ta Afrika.

Kasar Gabon na raba iyaka da Congo Brazzaville, Kamaru da kuma Equatorial Guinea. Bisa ga babban bankin duniya a 2017, kasar Gabon na da kimanin mutane sama da miliyan biyu.

Kaso 80 na mutanen kasa Kiristoci ne yayinda Musulman kasar suka kasance kaso 20.

Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da Gabon

Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da Gabon
Source: UGC

Harkar siyasar kasar Gabon ya daidaita tun bayan samun yancin kanta a 1960 sannan kuma shugabannin kasa uku kawai ta samu tsawon wannan lokaci, inda biyu daga cikinsu suka fito daga gida daya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: INEC ta gabatar da adadin masu zabe da aka yiwa rijista ga jam’iyyu siyasa

Bayan shugaba Leon M’Ba, Omar Bongo yakarbi mulki a 1967 sannan yayi ulki tsawon shekaru 41, wanda hakan yasa yayi shugabanci mafi tsawo a nahiyar Afrika ta yau.

A lokacin da ya mutu a shekarar 2009, sai aka zabi dansa Ali, sannan ya sake lashe zango na biyu a 2016 koda dai sakamakon ya haa hamayya, inda hakan ya jefa kasar a rikicin bayan zabe.

Ali Bongo dan shekara 59 ya samu dacutar shanyewar jiki a ranar 24 ga watan Oktoba yayinda ya ke a kasar Saudiyya sannan tun lokacin bai dawo Gabon ba, inda yake samun sauki a kasar Morocco.

Tun bayan faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya a 2015 sai tattalin arzikin kasar mai albarkatun man fetur ya shiga wani hali inda aka samu rashin aiki, shiga yajin aiki akai-akai, kamfanoni suka fara zuwa kasa, tare da daukan tsauraran matakai kan ma’aikata.

Bayan karban mulki, Ali Bongo ya kaddamar da wasu ayyuka kamar su asibitoci, hanyoyi da sauransu inda aka dakatar saboda rashin kudade.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel