Mutanen Kano su ne za su zama EFCC da ICPC a zaben 2019 - inji Kwankwaso

Mutanen Kano su ne za su zama EFCC da ICPC a zaben 2019 - inji Kwankwaso

Mun samu labari cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya caccaki gwamna mai-ci, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a kan zargin karbar cin hanci na makudan daloli.

Mutanen Kano su ne za su zama EFCC da ICPC a zaben 2019 - inji Kwankwaso

Kwankwaso yayi kira ga jama’a su zabi PDP a Jam'iyyar 2019
Source: Twitter

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa jama’an jihar Kano su ne za zama jami’an da za su yi yaki da cin hanci da rashawa a zaben da za ayi bana. Sanatan ya nuna cewa Talakawan jihar ne za su yi aikin hukumar EFCC da ICPC.

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya kara bayyana cewa zargin da ke wuyan gwamna Dr. Ganduje ya jawowa jama’ar Kano bacin-suna inda kowa a Duniya yake yi wa mutanen jihar kallon cewa su na karbar kudin rashawa.

KU KARANTA: Ganduje ya bada kwangilar gina bangaren maganin cutar kansa

Kwankwaso yayi wannan jawabi ne a lokacin da aka yi wani taron PDP na yakin neman zaben gwamna a Garin Kabo a karshen makon da ya wuce. Sanatan na Kano yayi kira ga mutanen jihar su zabi jam’iyyar PDP a bana.

Kwanaki Injiniya Rabiu Kwankwaso wanda yake wakiltar jihar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ya bayyana cewa zargin da ke yawo na cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya karbi rashawa zai jawowa APC bakin jini ainun.

Ana zargin cewa gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi makudan daloli daga hannun ‘yan kwangila. Sai dai har yanzu hukuma ba ta dauki wani kwakkaran mataki game da zargin da gwamnan ya musanya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel