2019: 'Yan Najeriya Miliyan 84 ke da rajistar zabe - INEC

2019: 'Yan Najeriya Miliyan 84 ke da rajistar zabe - INEC

Hukumar zabe ta kasa watau INEC, Independent National Electoral Commission, ta bayyana jimilla ta adadin 'yan Najeriya da a halin yanzu suke cikin shirin jefa kuri'un su a yayin babban zaben kasa na 2019 da za a gudanar a watan gobe.

Babbar hukumar zabe ta kasa da aka fi sani da hukumar INEC, ta bayyana cewa, a halin yanzu 'yan Najeriya miliyan 84 ke da rajista ta tabbatar da 'yancin tare cancantar kada kuri'unsu yayin babban zaben kasa na 2019.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmous Yakubu, shine ya bayar da shaidar hakan a yau Litinin yayin zaman ganawa da shugabannin jam'iyyun kasar nan cikin babban birnin tarayya na Abuja.

Cikin jawaban da Farfesa Yakubu ya gabatar, ya ce akwai Mutane 84,004,084 na adadin al'ummar kasar nan da ke da cikakkiyar cancanta ta kada kuri'un su a zaben kasa sakamakon rajistar zabe da suka riga da yi.

Shugaban Hukumar Zabe; Farfesa Mahmoud Yakubu

Shugaban Hukumar Zabe; Farfesa Mahmoud Yakubu
Source: Depositphotos

Wannan sanarwa ta biyo bayan tsare-tsaren da hukumar zabe ta shimfida domin babban zaben kasa da zai gudana cikin abinda bai wuci kwanaki arba'in ma su gabatowa.

Tun a bara hukumar zabe yayin fidda jadawalin ta na tsare-tsaren zabe, ta kayyade ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kujerar shugaban kasa da kuma ta 'yan majalisun dokoki na tarayya.

KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Hukumar sojin kasa ta yi kasafin N6bn domin sayen makamai a 2019

Kazalika hukumar ta kayyade ranar Asabar 2 ga watan Maris, 2019, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben gwamnoni da kuma 'yan majalisun dokoki na jihohin kasar nan.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, domin kyautatawa al'umma hukumar zabe ta kasa ta ce, za a ci gaba da karbar katin zabe cikin jihohi 36 da ke fadin kasar nan zuwa gabanin mako daya da gudanar zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel