Tsaro: Rundunar soji ta mika mutane 71 ga rundunar 'yan sanda a Adamawa

Tsaro: Rundunar soji ta mika mutane 71 ga rundunar 'yan sanda a Adamawa

- Birgediya janar Bello Mohammed na rundunar soji ta 23 ya mika damka mutane 71 da suka kama ga rundunar 'yan sanda

- Dakarun soji sun kama mutanen ne bisa zarginsu da hannu a rikicin kabilanci da ya barke a jihar

- Da yake karbar masu laifin, mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abu Vocho, ya jaddada aniyar rundunar 'yan sanda na tabbatar da tsaro a fadin jihar

A kalla mutane 71, da ake zargi da hannu a rikicin kabilanci da ya barke tsakanin mazauna garin Waja da Luguda a karamar hukumar Lamurde, rundunar soji ta mika hannun rundunar 'yan sanda a jihar Adamawa.

Birgediya janar Bello Mohammed, kwamandan rundunar soji ta 23 dake Adamawa, ne ya damka mutanen a hannun Abu Vocho, mataimakin kwamishinan 'yan sanda.

Tsaro: Rundunar soji ta mika mutane 71 ga rundunar 'yan sanda a Adamawa

Tsaro: Rundunar soji ta mika mutane 71 ga rundunar 'yan sanda a Adamawa
Source: Facebook

Majiyar Legit.ng ta rawaito cewar rikici tsakanin garuruwan Waja da Luguda dake karamar hukumar Lamurde a ranar 1 ga watan Janairu na sabuwar shekarar nan.

Da yake jawabi yayin karbar mutanen, Vocho ya jaddada aniyar rundunar 'yan sanda na tabbatar da tsaro a fadin jihar Adamawa.

A kwanakin baya ne dakarun sojin Najeriya na runduna ta 23 dake garin Yola, babban birnin jihar Adamawa, suka kama wasu mutane 71 da take zargi na da hannu a rikicin da ya barke tsakanin garuruwan Lunguda da Waja a Guyuk ta karamar hukumar Lamurde.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace daliban jami'a 9 a Katsina

Birgediya janar Bello Mohammed, kwamandan rundunar sojin da ya jagoranci ofireshon din kama mutanen, ya sanar da hakan a yau, Alhamis, yayin mika mutanen ga rundunar 'yan sanda.

Bello, ya kara da cewar an kara tura wasu dakarun soji zuwa yankin domin kara tabbatar da cewar wani rikicin bai kara barkewa ba tare da bayyana cewar sun yi nasarar kama wasu makamai da suka hada da bindigu, kwari da baka, adda, da wukake a wurin wadanda suka kama.

Da yake jawabi a kan muhimmancin zaman lafiya a tsakanin kabilun jihar, Bello ya ce rundunar soji a shirye take ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya.

Kazalika ya nemi hadin kan jama'a domin bawa dakarun sojin damar tabbatar da zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

An yi asarar amfanin gona da gidaje yayin rikicin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel