Na baiwa Tinubu ragamar shugabantan yakin neman zabena - Buhari yayinda ya rantsar da kwamitin kamfen APC

Na baiwa Tinubu ragamar shugabantan yakin neman zabena - Buhari yayinda ya rantsar da kwamitin kamfen APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasansa a ranan Litinin, 7 ga watan Junairu, 2019 a farfajiyar taron International Conference Centre ICC dake birnin tarayya, Abuja.

Shugaban kasan yace gudun kada yakin neman zabe ya dauke masa hankali daga harkan shugabancin al'umma, ya nada babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, matsayin wanda zai ja ragamar yakin neman zaben.

Buhari ya bayyana cewa za'ayi kamfen ne kan namijin ayyukan da gwamnatin tayi a shekaru uku da rabi da suka gabata kuma za'a fara da jihar Bauchi ranan Alhamis.

Na baiwa Tinubu ragamar shugabantan yakin neman zabena - Buhari yayinda ya rantsar da kwamitin kamfen APC

Na baiwa Tinubu ragamar shugabantan yakin neman zabena - Buhari yayinda ya rantsar da kwamitin kamfen APC
Source: UGC

KU KARANTA: Kotu ta haramtawa jam'iyyar APC gabatar da dan takaran gwamna a 2019

Ya yi kira ga mambobin kwamitin yakin neman zaben cewa kada su bari yadda jam'iyyun adawa ke sukarsu ya dauke musu hankali. Kawai su bayyana banbanci tsakanin 2015 da yau wajen yaki da rashawa, tattalin arziki da tsaro.

Wadanda suka halarci wannan taron sunw mataimkain shugaban kasa, Yemi Osinbajo; shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole; gwamnonin jam'iyyar, ministoci, da wasu manyan jami'an gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel