Yadda sojoji suka yi mana duka suka kuma kwace wayoyinmu kan zargin sata – Matasa

Yadda sojoji suka yi mana duka suka kuma kwace wayoyinmu kan zargin sata – Matasa

Wasu yan uwa biyu, Aregbesola Warif mai shekara 16 da Aregbesola Quadris, sun shad a kyar a hannun wasu da ake zargin jami’an hukumar sojin Najeriya ne kan zargin sace waya, a yankin Maryland da ke jihar Lagas.

Yan uwan biyu tare da wasu abokansu biyu na a hanyar su ta dawowa daga kantin siyayya na Ikeja, inda suka je shakatawa a ranar 1 ga watan Janairu.

Sai dai murnarsu ta koma bakin ciki yayinda suke gab da shiga wata motar haya da zai je hanyar Onipanu, lokacin da daya daga cikin fasinjojin yayi zargin cewa Quardri ya sace masa wayarsa.

A wani hirta da shi, Quardi wanda har yanzu yake cikin radadin ciwo ya yi bayanin ana aka kusa kashe shi.

Yadda sojoji suka yi mana duka suka kuma kwace wayoyinmu kan zargin sata – Matasa

Yadda sojoji suka yi mana duka suka kuma kwace wayoyinmu kan zargin sata – Matasa
Source: Depositphotos

Yace: “A lokacin da na shiga mota,sai na ga cewa wurin zaman mutum daya ya rage sai na shiga domin na hadu dad an uwana da abokaina. Sai daya daga cikin fasinjojin yace na sace mai wayarsa sannanya rike ni. Lokacin da dan uwana yayi kokarin shiga lamarin, sai suka fara dukanshi inda suka zarge su cewa yan kungiyana ne. Biyu daga cikinsu suka je kiran iyayenmu, inda suka bar dan uwana sai na fara neman ceto a taron jama’an.

“Sai sojoji biyu suka zo, kuma ba tare da sun nemi abunda ya faru ba, sai suka far mana suka daure mana hanayenmu sannan suka fara dukanmu.

“Jim kadan sai mahaifiyarmu ta kira wayana domin neman sanin abunda ya faru sai daya daga cikin sojojin yace mata mun yi sata ne. Sai tace ma sojojin tana nan zuwa inda muke, cewa su jira ta. Amma anan take bayan kiran wayan sau suka chanja ra’ayin su akan mu cewa su dauke mu zuwa sansaninsu.

“Sai suka kwace wayoyinmu suka cire sim din sannan suka bamu, sannan suka mikawayoiyinmu biyu ga wanda ya zarge mu da satar waya sannan kowa ya kama gabansa.

“Bayan kwanaki uku da na farfado daga dukan, daya daga cikin yan uwana, wanda ya gane daya daga cikin sojojin sai ya dauki iyayena zuwa gidansa amma ba a same shi a gida ba.

KU KARANTA KUMA: Babu kasar da aka ci amanarta kamar Najeriya a duniya - Buhari

“Iyayena sun kai rahoton lamarin ga ofishin yan sandan Alade, inda aka gayyaci daya daga cikin wadand suka dake mu. Ya amsa a gaban yan sandan cewa ya karbi wayoyinmu.

“Sai yan sandan suka fada masa cewa abunda yayi daukar doka ne a hannu, cewa da ya sani ya nemi jin ba’asi, a yanzu maganar nan da nake yi ba a dawo mana da wayoyinmu ba."

Lokacin da aka tuntubi kakakin yan sandan Lagas, Chike Oti ya tabbatar da samun kira kan wani hargitsi a ranar 1 ga watan Janairu, amma da aka isa wajen ba’a kowa ba. Yace za a yi bincike akan lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel