Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace daliban jami'a 9 a Katsina

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace daliban jami'a 9 a Katsina

Dalibai da mahukuntan jami'ar Al Qalam dake jihar Katsina sun shiga yanayin juyayi da damuwa bayan rahotnni dake yawo a gari sun bayyna cewar wasu 'yan bindiga sun sace daliban jami'ar a kalla 9 yayin hutun karshen mako.

Majiyar Legit.ng ta rawaito cewar 'yan bindigar sun kashe hudu daga cikin daliban da suka sace a gaba da da garin Kankara a kan hanyar zuwa Dutsinma. Kazalika, 'yan bindigar na neman a basu miliyan N100m kudin fansar ragowar dalibai 5 dake hannunsu.

Kakakin jami'ar Al Qalam, Abubakar Atiku, ya shaidawa majiyar mu cewar ba zai iya tabbatar ko karyata labarin kisa da garkuwa da daliban ba saboda har yanzu daliban jami'ar da dama da suka tafi hutun kirsimeti da sabuwar shekara basu dawo ba.

Atiku ya kara da cewar jami'ar na duba yiwuwar sanar da jami'an tsaro duk da har yanzu iyayen yaran basu tuntube su ko sanar dasu labarin garkuwa da daliban ba.

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace daliban jami'a 9 a Katsina

'Yan bindiga sun sace daliban jami'a 9 a Katsina
Source: Facebook

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Katsina, DSP Isah Gambo, ya ce babu daya daga cikin ofishin 'yan sanda 4 dake Kankara da Batagarawa masu makobtaka da jami'ar Al Qalam da suka samu rahoton satar daliban.

Ko a jiya sai da Legit.ng ta kawo maku labarin cewar rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta sanar da mutuwar wani kasurgumin dan fashi, Kane Mohammed, da aka fi sani da 'Dan mai-keke'.

Wannnan sanarwa na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya bawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau, Lahadi.

DUBA WANNAN: Buhari: PDP tayi taron ban mamaki a jihar Katsina, hotuna

Isa ya bayyana cewar jami'an rundunar 'yan sanda sun kashe kasurgumin dan fashin ne a ranar 4 ga watan Janairu yayin wani samame a maboyar 'yan ta'adda a yankin karamar hukumar Bakori.

A cewar kakakin, 'yan ta'addar ne suka fara kai wa tawagar jami'an 'yan sanda hari da muggan makamai har ta kai ga sun raunata dan sanda guda.

Ko a ranar ranar Laraba da ta gabata saida Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya sanar da cewa 'yan ta'adda sun mamaye sassa da dama na jihar a wurin taron gaggawa na masu ruwa tsaki a fanin tsaro inda ya ce mutanen jihar sunan cikin hadari har ma da shi.

A yayin da ya ke yiwa manema labarai bayanin wasu abubuwan da aka tattauwa wurin taron, sakataren gwamnatin jihar, Fr. Mustapha Mohammed Inuwa ya gargadin cewa akwai yiwuwar ba za ayi zabe a kananan hukumomi 8 ba muddin ba a dauki mataki ba kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Kananan hukumomin da ya ce 'yan ta'adda da barayin shanu sun mamaye a jihar sun hada da Jibia, Batsari, Safana, Dan-Musa, Faskari, Sabuwa, Dandume, Kankara da wasu sassan Kafur wadda itace karamar hukumar da gwamna ya fito daga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel