Da duminsa: Kotu ta haramtawa jam'iyyar APC gabatar da dan takaran gwamna a 2019

Da duminsa: Kotu ta haramtawa jam'iyyar APC gabatar da dan takaran gwamna a 2019

Babban kotun tarayya dake zaune a garin fatakwal, jihar Ribas ta yanke hukucin haramtawa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC gabatar da dan takaran gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Tonye Cole.

Kana, kotun ta haramta gabatar da sunan Sanata Magnus Abe wanda ya kai kara kotu. Wannan na nuna cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba tada dan takaran gwamnan jihar Ribas a zaben 2019 da za'ayi a watan Maris.

Bugu da kari, kotun ta yi watsi da zaben kato bayan kato da kuma na deleget da bangarorin jam'iyyar biyu suka gudanar a shekarar 2018.

Alkali mai Shari'a. Jastis James Omotosho, yayinda gabatar da shari'ar a Fatakwal yace babu zaben fidda gwanin da aka gabatar bisa ga doka.

KU KARANTA: Hankulan jama'a sun tashi yayinda tayan jirgi ya fashe da fasinjoji cike a Abuja

Mun kawo muku a baya cewa rikicin Jam'iyyar APC mai adawa a Jihar Ribas na kara cabewa. A halin yanzu tsohon Gwamna Rotimi Amaechi da Sanata Magnus Abe an ja daga.

Mun fahimci cewa asalin rikicin ya fara ne a dalilin kujerar Gwamna da Sanata Magnus Abe yake hari. Tsohon Gwamnan Jihar ba ya goyon bayan wannan yunkurin na Sanatan duk da cewa ana ganin shi ya shigo da shi cikin siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel