EFCC ta gabatar wa ministan shari’a da duk wasu takardu kan Diezani

EFCC ta gabatar wa ministan shari’a da duk wasu takardu kan Diezani

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gabatar da takardu kan tsohuwar ministar man fetur Misis Diezani Aliso-Madueke a gaban babban alkalin alkalai na Najeriya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN).

Baya ga rahoton cikakken bincike akan tsohuwar ministar, takardun hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa sun hada da na neman ta ruwa a jallo da kungiyar yan sandan kasashen waje wato Police Organization (INTERPOL), ke yi da kuma na wani hukuncin kotu da ta mallakawa gwamnati wasu kadarorin Misis Alison Madueke.

A cewar wata majiya wacce ta nemi a boye sunanta, tace za a fara shari’an nan ba da jimawa ba.

EFCC ta gabatar wa ministan shari’a da duk wasu takardu kan Diezani

EFCC ta gabatar wa ministan shari’a da duk wasu takardu kan Diezani
Source: Depositphotos

Majiyar tace: “Muna shirye-shiryen dawo da tsohuwar ministar man fetur din daga kasar Ingila. Hukumar EFCC ta dauki lamarin dawo da ita da muhimmanci a 2019.

KU KARANTA KUMA: Babu kasar da aka ci amanarta kamar Najeriya a duniya - Buhari

“Mun gabatar da duk takardun da ya kamata a gaban ministan shari’a, ciki harda rahoton bincike, hukuncin kotu kan kadarorin Diezani da aka kwace, hukuncin kotu akan wasu da ake zarginsu tare da kuma rahoton INTERPOL akan ta.

“Ta rigada ta rasa wasu kadarorinta. Kadaroroin tsohuwar ministar da aka mallakawa gwamnati sun hada da wani ginin bene a Banana Island, Lagas, wani gida mai sashi shida a Ikoyi da kuma wani gida a Yaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel