Rashin tsaro: Hukumar sojin kasa ta yi kasafin N6bn domin sayen makamai a 2019

Rashin tsaro: Hukumar sojin kasa ta yi kasafin N6bn domin sayen makamai a 2019

Hukumar sojin kasa ta Najeriya ta shirya batar da kimanin Naira biliyan shida wajen sayen makamai da kayayyakin aiki na gudanawarta a shekarar bana ta 2019 domin ci gaba da yakar ta'addanci musamman a yankin Arewa maso Gabas.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar sojin kasa ta Najeriya ta yi kasafi na tsare-tsaren batar da Naira Biliyan shida a bana wajen sayen makamai da kayan aiki domin ci gaba da tunkarar masu tayar da kayar baya na Boko Haram da sauran harkokin tsaro a kasar nan.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan kasafi na Naira Biliyan shida da hukumar dakarun sojin ta tsara na cikin babban kasafin kudin kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a zauren majalisar tarayya a watan Dasumba na shekarar 2018 da ta gabata.

Shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya; Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai

Shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya; Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai
Source: Depositphotos

Wannan kasafi na N6bn ba ya daga cikin Dalar Amurka biliyan 1 na rarar kudin man fetur da shugaban kasa Buhari ya yi alkawarin bai wa hukumar dakarun sojin Najeriya domin bunkasa harkokin tsaro a yankunan Arewa maso Gabas tun a watan Dasumba na shekarar 2017.

KARANTA KUMA: Yadda Aisha Buhari ta bogi ta yiwa wani kamfani damfarar N150m

Sai dai cikin wani rahoto da kakakin hukumar sojin kasa na Najeriya ya aike zuwa ga manema labarai tun a watan Dasumba na bara, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, ya ce har ila yau wannan kudade ba su iso hannun hukumar ba.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, kasafin hukumar sojin ya yi shirin batar da Naira Biliyan shida wajen tanadar dukkanin ababe domin jin dadin dakaru da kuma inganta harkokin su na gudanarwa kama daga makamai, gine-gine, motocin sufuri, kayayyakin lafiya da makamantansu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel