Yanzu Yanzu: Babban sakataren labaran Yahaya Bello ya yi murabus

Yanzu Yanzu: Babban sakataren labaran Yahaya Bello ya yi murabus

- Babban sakataren labaran Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi , Petra Akinti Onyegbule, ma ya ajiye aiki a safiyar ranar Litinin, 7 ga watan Janairu

- Har yanzu babu wani cikakken bayani kan wannan mataki da ya dauka

- Ana zargin murabus din Onyegbule baya rasa nasaba da zargin kusancinsa da Frank Shaibu, babban hadimin Atiku Abubakar

Kasa da wata daya da babban hadimin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi akan labarai, Joel Odaudu, ya ajiye mukaminsa, babban sakataren labaransa, Petra Akinti Onyegbule, ma ya ajiye aiki a safiyar ranar Litinin, 7 ga watan Janairu.

Jaridar Independent ta rahoto cewa har yanzu ba a san dalilin yin murabus dinsa ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Yanzu Yanzu: Babban sakataren labaran Yahaya Bello ya yi murabus

Yanzu Yanzu: Babban sakataren labaran Yahaya Bello ya yi murabus
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa murabus din Onyegbule baya rasa nasaba da zargin kusancinsa da Frank Shaibu, babban hadimin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Alhaji Atiku Abubakar.

A halin da ake ciki, Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zabe mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar zai kaddamar da kamfen dinsa a Lokoja, babbar birin jihar Kogi a yau Litinin, 7 ga watan Janairu.

Mista Bode Ogunmola, kakakin jam’iyyar PDP a jihar Kogi kuma sakataren labarai na kungiyar kamfen din jam’iyyar a jihar, ne ya bayyana hakan.

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole Aisha Buhari ta yi bayanin abunda ya faru da masu hana ruwa gudu a Aso Rock - Fayose

Yace an kammala duk wani tsare-tsare domin ganin anyi kamfen din cikin nasara a babban filin wasa na Lokoja Confluence Stadium.

Ya kara da cewa an magance maganganun da ya taso kan amfani dsa filin wasan sannan kuma cewa gwamnatin jihar ta amince da amfani da kayayyakin don takarar kamfen dinta na shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel