Yanzu-yanzu: Mun damke sojojin da sukayi juyin mulki da safen nan - Gwamnatin jihar Gabon

Yanzu-yanzu: Mun damke sojojin da sukayi juyin mulki da safen nan - Gwamnatin jihar Gabon

Gwamnatin jihar Gabon ta alanta cewa tana nan daram dam-dam bayan wasu jami'an sojin kasar sun yiwa shugaban kasan juyin mulki da safen nan.

Kakakin gwamnatin, Guy-Bertrand Mapangou ya bayyanawa AFP cewa sun damke da yawa daga cikin sojojin da ke hannu cikin juyin mulkin.

Yace: "Komai ya daidaita yanzu, mun shawo kan al'amarin. Daga cikin sojoji biyar da sukayi wannan abu, mun damke hudu. Dayan ya gudu."

KU KARANTA: Yadda Dino Melaye ya fito daga gidansa, ya zube warwas a kasa kamar zai mutu

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa sojoji a kasar Gabon sun kifar da gwamnatin kasar. Rundunar sojin kasar sun mamaye gidan rediyon da ke Gabon inda su ke ta sukar halin da shugaban kasa Ali Bango yake ciki.

Wasu Dakarun Soji a Gabon sun shiga babban gidan rediyon da ake da shi a kasar inda su ka tabbatar da kifar da gwamnati mai-ci. Manema labarai sun tabbatar da cewa an ji harbe-harben bindigogi a babban birnin Libreville dazu da sassafe.

Sojojin kasar na Gabon sun sanar da cewa za su kafa shugabanci na rikon kwarya inda za a nada wata majalisa ta musamman da za ta ja ragamar kasar. Sojojin sun ce za su dawo da mulkin farar hula ne bayan hambarar da gwamnatin Bongo.

Yanzu haka Ali Bongo yana kasar Morocco inda yake fama da rashin lafiya tun shekarar bara. A farkon shekarar nan ne shugaban kasar mai shekaru 59 ya aikowa mutanen kasar Gabon sako tun bayan da ya fadi da lalurar rashin lafiya a bara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel