Buhari ya zabge fiye da N14bn daga kasafin majalisa

Buhari ya zabge fiye da N14bn daga kasafin majalisa

Shugaba Muhammadu Buhari ya rage zunzurutun kudin Naira Biliyan 145 daga cikin kason majalisa a kasafin kudin shekarar 2019 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A shekarar 2018 da ta gabata, majalisar ta samu Naira Biliyan 139.5 a kasafin kudi amma a wannan shekarar shugaban kasar ya gabatarwa majalisar da Naira Bilyan 125 wanda hakan ke nuna ya rage Naira Biliyan 14.5.

An kwashe shakaru masu yawa ba tare da sanin kason da majalisa ke samu ba a kasafin kudi har sai a shekarar 2017 da majalisar ta bayyana kason na ta sakamakon matsin lamba da al'ummar kasa suka rika yi mata.

Buhari ya zabge fiye da N14bn daga kasafin majalisa

Buhari ya zabge fiye da N14bn daga kasafin majalisa
Source: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan ta'addan sun kwace iko da kananan hukumomi 8 a jihar Katsina

A baya, shugaban kasar ya gabatarwa majalisar N125 biliyan a matsayin kason su a shekarar 2018 amma 'yan majalisar suka kara kudin ya kai N139bn wadda hakan bai yiwa fadar shugaban kasae dadi ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar kasafin kudin na majalisar ta karu daga N19 biliyan a shekarar 2000 har ya kai zuwa N150 biliyan. Daga shekarar 2010 zuwa 2013, majalisar ta rika karbar N15o biliyan a duk shekara.

Kafin zuwan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, kasafin kudin majalisar ya kai N120 biliyan amma bayan ya hau mulki ya rage kudin zuwa N115 biliyan a shekarar 2016 kuma majalisar ta amince da hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel