Ganduje ya bada kwangilar Biliyan 2.4 a asibitin Muhammadu Buhari

Ganduje ya bada kwangilar Biliyan 2.4 a asibitin Muhammadu Buhari

Mun samu labari cewa Gwamnatin jihar Kano ta bada kwangilar makudan kudi domin gina cibiya ta musamman mai kula da cutar kansa a katafaren asibitin kwararrun nan da aka gina a jihar kwanaki.

Ganduje ya bada kwangilar Biliyan 2.4 a asibitin Muhammadu Buhari

Gwamnan Kano ya bada kwangilar gina bangaren maganin cutar kansa
Source: Twitter

Gwamna Abdullahi Ganduje ya bada kwangilar Naira biliyan 2.4 domin gina bangaren cutar kansa a asibitin Muhammadu Buhari da ke Kano. Gwamnan ya bayyana cewa wani kamfanin kasar waje ne za su rika lura da wannan aiki.

Kamar yadda labari ya zo mana daga jaridar Daily Trust, kamfanin Varian Medicals na kasar waje ne za su tsaya su tabbatar wajen ganin an yi wannan aiki yadda ya kamata. Gwamnan yace za ayi aiki kamar yadda ake yi a kasashen Turai.

KU KARANTA: Abin da Buhari yayi wa Shagari bai yi masa dadi ba - Iyalin Marigayi

Idan har aka kammala wannan aiki, Kano za ta shiga sahun irin su cibiyar Peter MacCallum Melbourne da ke kasar Australia inda ake da asibiti dauke da dakin bincike domin maganin cutar kansa mai lahanta kwayoyin ran mutum.

Gwamnatin jihar ta Kano ta bayyana cewa za a kawo manyan na’urorin da ke kashe kwayoyin kansa a jikin Dan Adam da kuma duk wasu kayan aiki da ake bukata wajen maganin cutar ta kansa da ke addabar jama’a a ko ina a Duniya.

Mai Girma Dr. Abdullahi Ganduje ya bada wannan aiki ne a sakamakon dinbin mutanen da ke mutuwa saboda cutar a Arewacin Najeriya inda ake da dinbin jama’a. Babu irin wannan asibiti a Arewa sai an je Garin Abuja an kashe makudan kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel