2019: Atiku zai kai kamfen dinsa Kogi a yau, Litinin, 7 ga watan Janairu

2019: Atiku zai kai kamfen dinsa Kogi a yau, Litinin, 7 ga watan Janairu

- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar zai kaddamar da kamfen dinsa a Lokoja, babbar birin jihar Kogi

- Zai kaddamar da kamfen din ne a yau Litinin, 7 ga watan Janairu

- An kammala duk wani tsare-tsare domin ganin anyi kamfen din cikin nasara a babban filin wasa na Lokoja Confluence Stadium

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zabe mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar zai kaddamar da kamfen dinsa a Lokoja, babbar birin jihar Kogi a yau Litinin, 7 ga watan Janairu.

Mista Bode Ogunmola, kakakin jam’iyyar PDP a jihar Kogi kuma sakataren labarai na kungiyar kamfen din jam’iyyar a jihar, ne ya bayyana hakan.

2019: Atiku zai kai kamfen dinsa Kogi a yau, Litinin, 7 ga watan Janairu

2019: Atiku zai kai kamfen dinsa Kogi a yau, Litinin, 7 ga watan Janairu
Source: Facebook

Bisa ga jaridar Daily Trust, yace an kammala duk wani tsare-tsare domin ganin anyi kamfen din cikin nasara a babban filin wasa na Lokoja Confluence Stadium.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa muka kai mamaya gidan jaridar Daily Trust – Sojoji

Ya kara da cewa an magance maganganun da ya taso kan amfani dsa filin wasan sannan kuma cewa gwamnatin jihar ta amince da amfani da kayayyakin don takarar kamfen dinta na shugaban kasa.

A wani lamari na daban, mun ji cewa ‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Peter Obi, yayi magana game da jita-jitar da ke yawo na cewa babu hadin kai tsakanin manyan kusoshin PDP da ke Kudu maso gabashin Najeriya yayin da ake shirin zabe.

Peter Obi ya tabbatar da cewa babu wata sa-in-sa a jam’iyyar PDP a yankin na Kudancin kasar. Obi ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da wasu manyan malaman addinin kirista jiya a cikin Garin Awka a jihar Anambra.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel