Mataimakin Shugaban kasa ya yi ganawar sirri da Sarkin Awujale

Mataimakin Shugaban kasa ya yi ganawar sirri da Sarkin Awujale

- Mataimakin shugaba kasa Osinbajo ya yi ganawar sirri a Sarkin Awujale, Oba Siriki Adetona

- Ganawar ta gudana yayin da Osinbajo ke shawagin neman goyon bayan al'ummar kasar nan yayin da babban zabe ya gabato

- An yiwa manema labarai haramci na ko leke tare da cewa lamarin bai shalle su ba

Mun samu cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, yayi ganawar sirri da babban Basaraken Masarautar Ijebu ta Awujale, Oba Siriku Adetona a gidan sa da ke garin Ijebuode.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ganawar da ta gudana tsawon sa'o'i biyu, inda aka yiwa manema labarai haramci na ko leke tare da shaida ma su cewa ganawa ce da ba ta shafe su ba.

Hakan bai sanya manema labarai sun gaza yada rahoto da cewa, akwai yiwuwar ganawar ta gudana ne domin neman goyon Basaraken da kuma makarraban fadarsa baki daya yayin da babban zaben kasa ya gabato.

Mataimakin Shugaban kasa ya yi ganawar sirri da Sarkin Awujale

Mataimakin Shugaban kasa ya yi ganawar sirri da Sarkin Awujale
Source: UGC

A ranar Asabar din da ta gabata, mataimakin shugaban ya ci gaba da gudanar da yakin sa na neman zabe na gida zuwa gida a garin Saki da ke jihar Oyo a Kudancin kasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin shugaban kasar yayin shawagin sa na neman goyon baya, ya kuma gabatar da jawabai ga dumbin al'umma cikin annashuwa da ya sanya annuri a fuskokin su.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai yiwa dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC yakin neman zabe - Garba Shehu

Kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito cewa, tawagar mataimakin shugaban kasar ta hadar da mataimakin gwamnan jihar Oyo, Moses Alake Adeyemo, Ministan Sadarwa Adebayo Shittu, da kuma dan takarar kujerar gwamna na jihar a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, Adebayo Adelabu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel