Gwamnan Ebonyi Umahi ya canzawa wasu kwamishinonin sa wurin aiki

Gwamnan Ebonyi Umahi ya canzawa wasu kwamishinonin sa wurin aiki

Mun samu labari daga jaridar Daily Trust ta kasar nan cewa Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi yayi wasu canji a gwamnatin sa inda aka ga ya sauyawa wasu Kwamishinoni mukaman su kwanan nan.

Gwamnan Ebonyi Umahi ya canzawa wasu kwamishinonin sa wurin aiki

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya nada wasu kwamishinoni
Source: Depositphotos

A Ranar Lahadi ne David Umahi ya girgiza gwamnatin sa yayin da ya raba ma’aikatar raba filaye da gidaje zuwa 2. Yanzu haka kowace ma’aikata za ta rike kwamishinan ta na dabam inji mai girma Gwamnan jihar na Ebonyi.

Sunday Inyima, wanda yake rike da ma’aikatar da ke lura da kan iyakokin jihar shi ne zai kula da sabuwar ma’aikatar gidaje da raye birane da aka kafa. Farfesa John Ekeh kuma shi ne zai cigaba da rike ma’aikatar raba filaye na jihar.

KU KARANTA: 2019 sabon rikici ya farraka kan jiga-jigan jam'iyyar APC

Babban Sakataren yada labarai na gwamnan jihar Ebonyi watau Emmanuel Uzor, shi ne ya bayyana wannan a Ranar Lahadin nan. Ana sa rai cewa za a mikawa majalisar dokokin Ebonyi sunayen sababbin kwamishinonin jihar.

Uzor ya kuma bayyana cewa an game ofishin mai bada shawara kan harkar tsaro watau SSA-IS da kuma ma’aikatar da ke kula da harkokin kan iyakan jihar. Dr Kenneth Ugbala, shi ne wanda zai zama sabon kwamishinan ma’aikatar.

Kwanakin baya kun ji yadda David Umahi ya rabawa Kungiyar CAN da wasu malaman addini makudan kudi. Fastoci akalla 2500 ne su ka tashi da Miliyan guda domin su taya gwamnan da addu’o’in lashe zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel