Shugaba Buhari zai yiwa dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC yakin neman zabe - Garba Shehu

Shugaba Buhari zai yiwa dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC yakin neman zabe - Garba Shehu

- Shugaba Buhari zai taya dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC yakin neman zabe domin cimma nasara a kowane mataki

- Mallam Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ba ya da tantamar samun nasara a zaben 2019 sakamakon mashahurancin sa wurin al'ummar Najeriya

- Hadimin shugaban kasar ya ce taya sauran 'yan jam'iyyar APC yakin neman zaben ba zai hana shugaba Buhari sauke nauyin jagorancin kasar nan da ya rataya a wuyansa

Za ku ji cewa, fadar shugaban ta yi karin haske dangane da goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ga dukkanin ‘yan takara na jam’iyyar sa ta APC yayin babban zaben kasa da za a gudanar a bana.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, ko shakka ba bu shugaba Buhari zai taka muhimmiyar rawar gani wajen yiwa dukkanin ‘yan takarar jam'iyyarsa yakin neman zaben.

Kasancewar shugaba Buhari jagora kuma dan takara a jam'iyyar APC zai bayar da gudunmuwa ta yakin neman zabe ga dukkanin ‘yan takara na jam'iyyar sa domin cimma nasara a kowane mataki.

Shugaba Buhari zai yiwa dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC yakin neman zabe - Garba Shehu

Shugaba Buhari zai yiwa dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC yakin neman zabe - Garba Shehu
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, fadar ta bayyana wannan rahoto ne cikin wani sako da babban hadimi na mussaman ga shugaba Buhari kan hulda da manema labarai ya gabatar, Mallam Garba Shehu.

Mallam Garba Shehu yake cewa, wannan sha tara ta arziki da shugaba Buhari zai yiwa ‘yan takara na jam'iyyar sa ba zai kawo wata tangarda ba ko wani cikas wajen sauke nauyin jagorantar al'ummar kasar nan da ya rataya a wuyansa.

Cikin sanarwar da Mallam Shehu ya zayyana, shugaban kasa Buhari ba zai gaza ba wajen taya ‘yan takarar jam'iyyar sa yakin neman zaben da nuna goyon baya a duk yayin da suka nemi bukatar hakan.

KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da kudaden shiga na N30bn a shekarar 2018

Cikin bugun gaba da nuna fififko, Mallam Shehu ya ce a halin yanzu shugaba Buhari ba ya da wata fargaba ta samun nasara a zaben watan gobe sakamakon mashahurancin sa da ya yiwa na kowane mai da'awar shahara fintinkau da kece raini.

Sai dai hakan ba zai sanya ya gaza ba wajen ci gaba da neman goyon baya domin yiwa sauran ‘yan takara dukan koshi yayin nasara a zaben da za a gudanar makonni kadan ma su gabatowa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel