2019: An halaka dan jagaliyan siyasa saboda lika fastocin yan takara a Fatakwal

2019: An halaka dan jagaliyan siyasa saboda lika fastocin yan takara a Fatakwal

Duk da irin kiraye kirayen da ake yi ma jama’a, musamman ma matasa dake shiga bangar siyasa ko jagaliyar siyasa a game da yin taka tsantsan wajen salwantar da rayuwarsu ga yan siyasa yayin da zaben 2019 ke karatowa, amma wasu basa ji.

Legit.com ta samu rahoton wani matashi mai suna Chimezie Dike wanda ya gamu da ajalinsa a sakamakon wani rikici daya barke tsakaninsa da wasu mutane akan bahallatsar lika fastar wata yar mata dake takarar kujerar majalisar wakilai da ta daukeshi haya.

KU KARANTA: Tsuguni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun sace karamar yarinya tana dawowa daga Islamiya

2019: An halaka dan jagaliyan siyasa saboda lika fastocin yan takara a Fatakwal

Dan jagaliya Dike
Source: UGC

Dan jagaliyar siyasa, Dike ya mutu ne bayan da rikici ya kaure tsakaninsa da wata mata mai suna Ifeoma Ekeozor da danta Henry Ekeorzo, wanda suka nuna rashin amincewarsu da lika fastar yan siyasa da Dike yayi a bangon gidansu dake Lamba 40B, titin Azikwe dake unguwar Diubu cikin garin Fatakwal na jahar Ribas.

Wannan lamari ya faru ne a ranar da misalin karfe 8:20 na daren Asabar, sai dai wani abin mamakin shine ita yar takarar da Dike ke lika fastarta, Collyns Owondah yar jam’iyyar APC ce, haka nan ta ma matar da ta hana a lika mata fasta a bangon gida, ita ma yar APC ce, itace shugaban matan APC na unguwar Diobu.

Sanadiyyar tuburewar da bangarorin biyu suka yi inda Dike ke cewa sai ya lika fastar, ita kuma Ifeoma na cewa bai isa bane, ta kai ga an fara kokawa, ba tare da bata lokaci ba Henry ya shigar ma mahaifyarsa, nan da nan ya burma ma Dike wuka a kahon zuciya, nan take ya fadi matacce.

Wannan lamari ya tayar da hankulan matasan yankin, inda suka fusata suka shiga farfasa gidaje da dukiyoyin jama’an yankin, musamman ma gidan Uwargida Ifeanyi Ekeazor, wanda suka yi watsa watsa da kayan gidan gaba daya, tare da fasa gilasai da kofofi.

Daga karshe kaakakin rundunar Yansandan jahar, Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin, sa’annan ya bayyana cewa rundunarsu zata dauki dukkanin matakin daya dace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel