2019: Babu wani rashin jituwa a tafiyar PDP – Inji Peter Obi

2019: Babu wani rashin jituwa a tafiyar PDP – Inji Peter Obi

- Peter Obi yayi watsi da rade-radin rabuwar kai a cikin jam’iyyar PDP

- ‘Dan takarar yace kan ‘Yan PDP da ke kudu maso Gabas bai rabu ba

- Obi yace yawan kuri’un da PDP za ta samu a a yankin zai bada shaida

2019: Babu wani rashin jituwa a tafiyar PDP – Inji Peter Obi

Peter Obi yace babu masu yi wa APC aiki a PDP
Source: Twitter

‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Peter Obi, yayi magana game da jita-jitar da ke yawo na cewa babu hadin kai tsakanin manyan kusoshin PDP da ke Kudu maso gabashin Najeriya yayin da ake shirin zabe.

Peter Obi ya tabbatar da cewa babu wata sa-in-sa a jam’iyyar PDP a yankin na Kudancin kasar. Obi ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da wasu manyan malaman addinin kirista jiya a cikin Garin Awka a jihar Anambra.

KU KARANTA: Diyar David Mark ta kunyata mahaifin ta a Benue bayan ta bar PDP

‘Dan takaran na 2019 yace babu alaman gaskiya rade-radin da ake ta yadawa na cewa akwai wasu ‘yan PDP da ke shiryawa jam’iyyar zagon kasa. Obi yace ‘ya ‘yan PDP sun zama tamkar tsintsinya mai madauri guda a kudancin Najeriya.

Mista Peter Obi ya bada tabbacin cewa dukkanin ‘Ya ‘yan PDP su na aiki wajen ganin APC ta sha kasa a zaben da za yi bana. ‘Dan takaran ya sha alwashin nunawa jama’a yadda PDP za ta nemi nasara a zaben da za ayi a farkon shekarar nan.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kara da cewa, PDP za gyara kasar nan, ta kuma yi maganin rashin aikin yi tare da gina hanyoyi inda har yayi alkawarin gina gadar da ta hada Neja-Delta da yankin Kudu maso Gabas a cikin watanni 6.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel