Tsuguni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun sace karamar yarinya tana dawowa daga Islamiya

Tsuguni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun sace karamar yarinya tana dawowa daga Islamiya

Ayyukan yan bindiga da masu garkuwa da mutane na cigaba da ruruwa a jahar Zamfara da kewaye, duk kuwa da irin kokarin da gwamnatocin tarayya da na jahar Zamfara ke yi na ganin ta shawo kan matsalar, amma hakan na neman ci tura.

Anan ma Legit.com ne ta samu rahoton sace wata karamar yarinya yar Islamiya mai suna Fatima Musa, da wasu yan bindiga marasa Imani suka yi garkuwa da ita a daidai lokacin da take kan hanyar komawa gida daga makarantar Islamiyya.

KU KARANTA; Iyalan marigayi Shehu Shagari sun bayyana bacin rai game da yadda Buhari ya cutar da mahaifinsu

Tsuguni bata kare ba: Masu garkuwa da mutane sun sace karamar yarinya tana dawowa daga Islamiya

Fatima
Source: Facebook

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Bashir Hashim ne ya sanar da haka, inda yayi nuni da cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 6 ga watan Janairu a garin Gusau, babban birnin jahar Zamfara.

Daliba Fatima ba ita bace farau ba da yan bindiga suka fara sacewa a jahar Zamfara, jahar da tayi kaurin suna wajen fuskantar ayyukan yan bindiga da masu garkuwa da mutane, idan za’a tuna ko a kwanakin baya sai da yan bindiga suka yi awon gaba da wasu yan mata biyu tagwaye.

Yan bindigan sun saci tagwayen ne daga kauyensu, Dauran, a lokacin da suke kan hanyar zuwa gidajen yan uwa da abokan arziki don raba musu katunan gayyata zuwa bikinsu da za ayi nan bada jimawa ba, a wancan lokaci.

An shigha rudani sosai game da halin da yan matan ke ciki musamman a lokacin da yan bindigan suka yi barazanar kashe guda daga cikinsu idan har ba’a biyasu kudin fansa da suka sanyashi akan naira miliyan 100 ba.

Bayan doguwar tattaunawa tsakanin iyalan yan matan da yan bindigan an samu saukin kudin, inda suka yarda a basu naira miliyan goma sha biyar, da kyar aka hada kudin ta hanyar neman taimako da kuma wasu makudan miliyoyi da Sanata Kabiru Marafa ya taimaka musu dasu, daga karshe suka sakosu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel