An sake kwatawa: Gungun yan bindiga sun halaka mutum 5 a Kaduna

An sake kwatawa: Gungun yan bindiga sun halaka mutum 5 a Kaduna

Har yanzu tana kasa tana dabo game da matsalar tsaro a Arewacin Najeriya, inda anan ma an samu wasu gungun mahara yan bindiga da suka kai mummunar farmaki a wani kauye dake cikin karamar hukumar Birnin Gwari na jahar Kaduna.

Majiyar Lergit.com ta ruwaito yan bindigan sun diran ma kauyen Kwasakwasa ne dake kan babbar hanyar Birnin Gwari zuwa garin Funtua da misalin karfe 6 na yamma akan babura dauke da bindigu.

KU KARANTA: Iyalan marigayi Shehu Shagari sun bayyana bacin rai game da yadda Buhari ya cutar da mahaifinsu

Isarsu kauyen keda wuya sai bude ma jama’a wuta suka harbin mai kan uwa da wabi, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya tabbatar, inda yace a dalilin harbe harben da yan bindigan suka yi sun jikkata mutane bakwai wanda a yanzu haka suna asibiti.

Shaidan gani da idon ya bayyana cewa baya ga wadanda aka jikkata, yan bindigan sun kashe mutane biyar, daga cikinsu akwai yan asalin kauyen kwasakwasa gua biyu, yayin da sauran mutanen da aka kashe guda uku sun fito ne daga garin Sabon Layi akan hanyarsu ta dawowa daga daurin aure.

“Mun yi asarar mutane biyar da suka mutu a sanadiyyar bude wuta da yan bindiga suka yi mana, na tafi wani kauyen dake makwabtaka damu ne mai suna Raya Dan Auta a lokacin da jama’anmu suka yi kirani akan na kira jami’n tsaro cewa yan bindiga sun kai ma kauyenmu hari.

“Sai dai ko kafin zuwan Yansanda, tuni yan bindigan sun kashe mutane biyar, sun jikkata mutane bakwai, sun harbi mutanen ne a baya, wasu kuma a kafa, yayin da wasu kuma a hannu suka samesu. Haka zalika sun kona motoci guda biyu kirar Golf, sa’annan sun yi awon gaba da babura hudu.” Inji shi.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace mutane uku yan bindigan suka kashe ba biyar ba. Sa’annan ya bada tabbacin Yansanda zasu cigaba da kokarin kare al’umma da dukiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel