Za ayi garkuwa da gwamnonin jihohin Najeriya guda 5 – Wani Gwamna ya bayyana ma Sojoji

Za ayi garkuwa da gwamnonin jihohin Najeriya guda 5 – Wani Gwamna ya bayyana ma Sojoji

A daidai lokacin da zabukan gama gari na shekarar 2019 ke cigaba da kusantowa, gwamnatocin jihohi, kananan hukumomi da ta tarayya na yin iya bakin kokarinsu na ganin sun samar da isashshen tsaro tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro don kare lafiya da dukiyoyin mutane.

Saboda wannan lokacin ya yi daidai da lokacin da ake samun yawaitan ayyukan miyagun mutane, tsageru da masu tayar da kayar baya, inda anan ma gwamnan jahar Ebonyi dake kudu maso gabashin Najeriya, David Umahi ne ya bayyana barazanar da ake yi masa ga rundunar Sojin Najeriya.

KU KARANTA: Yiwa Buhari ihu a majalisa: Shehu Sani ya bayar da shaida a kan Dino Melaye

Za ayi garkuwa da gwamnonin jihohin Najeriya guda 5 – Wani Gwamna ya bayyana ma Sojoji

Gwamna Umahi
Source: UGC

Legit.com ta ruwaito Gwamna David Umahi ya bayyana cewa tsagerun kungiyar rajin kafa kasar Biyafara, IPOB, sun yi barazanar yin garkuwa da shi da sauran gwamnoni jihohin yankin guda hudu da suka hada da na Abia, Anambra, Imo da Enugu.

Gwamna Umahi ya bayyana haka ne yayin da rundunar Sojan kasa ke kaddamar da wani aikin tsaro na musamman a yankin kudu maso gabas da ta yi a barikin Sojoji dake garin Abakaliki, babban birnin jahar Ebonyi, mai taken ‘Operation Egwu Eke III’.

Bugu da kari gwamnan ya bayyana cewa IPOB ta yi masa wannan barazana ne ta wani sakon kar ta kwana da suka tura ma uwargidarsa, sa’annan ya tabbatar ma rundunar Sojin Najeriya cewa jahar Ebonyi bata cikin jihohin da suka samar da kasar Biyafara.

“Kun zo a daidai lokacin da yayan kungiyar IPOB suke aika mana da sakonin kar ta kwana na cewa ba zasu taba bari a gudanar da zaben 2019 ba, kuma suna hadawa da zagi tare da cin mutuncin shuwagabanni musamman gwamnoni.

“Kimanin kwanaki biyar da suka gabata suka aiko ma matata sakon waya cewa zasu yi garkuwa dani da sauran gwamnonin yankinmu guda hudu, kuma ba zasu sakemu ba har sai an biya kudin fansa akanmu, daga nan kuma su kashemu, su kashe kansu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel