Manyan Jam’iyyar PDP sun huro wuta sai an saki Sanata Dino Melaye

Manyan Jam’iyyar PDP sun huro wuta sai an saki Sanata Dino Melaye

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Jagororin jam’iyyar PDP a jihar Kogi sun nemi jami’an tsaro su yi maza su saki Sanatan jihar watau Dino Melaye wanda yake tsare a hannun ‘yan sandan Najeriya.

Manyan Jam’iyyar PDP sun huro wuta sai an saki Sanata Dino Melaye

PDP ta koka game da yadda 'Yan Sanda su ka dukunkuno Sanatan ta
Source: Facebook

Manyan jam’iyyar hamayya ta PDP a yammacin jihar Kogi sun yi kira ga ‘yan sanda su saki Sanata Dino Melaye da su ka tsare da zargin yunkurin kisan kai. Manyan ‘yan adawan sun yi wannan kira ne bayan wani taro da su kayi jiya Lahadi.

Jagororin jam’iyyar adawar sun yi wani zama na musamman ne a garin Iyah-Gbedde da ke cikin karamar hukumar Ijummu a karshen makon nan. A karshen wannan zama ne su ka cin ma matsaya cewa ya kamata a fito da Sanatan.

KU KARANTA: Shehu Sani ya ba da shaida a kan Sanata Dino Melaye a Majalisa

Shugaban PDP na yankin Kogi ta yamma inda Dino Melaye ya fito watau Taiwo Kola-Ojo ya sa hannu a madadin sauran ‘yan PDP na yankin inda Jam’iyyar tayi tir da yadda jami’an tsaro su ka kama babban ‘Dan majalisar kamar wata dabba.

Jami’an tsaro sun dauki tsawon kwana da kwanaki a gaban gidan ‘Dan majalisar su na nema su yi ram da shi. Sai bayan kusa mako guda ne ya iya shiga hannu. Shugabannin PDP na jihar sun nuna rashin jin dadin su ga yadda wannan abin ya auku.

Bayan nan kuma jam’iyyar hamayyar ta koka da yadda ake rusa allon takarar Sanatan tare da yunkurin ganin bayan rayuwar sa. Jam’iyyar adawar tace hakan na nuna cewa zaben 2019 ba zai yi kyau ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel