Siyasa rigar 'yanci: Diyar David Mark ta kunyata mahaifin ta a Benue

Siyasa rigar 'yanci: Diyar David Mark ta kunyata mahaifin ta a Benue

Daya daga cikin 'ya'yan tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Blessing Onuh ta sanar da ficewar ta daga jam'iyyar mahaifin ta Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA).

Blessing Onuh, wadda bayan sauya shekarar ta ta ta kuma samu tikitin yin takarar kujerar 'yar majalisar mazabar Otukpo/Ohimini a majalisar wakilai, ta bayyana tsohuwar jam'iyyar ta ta da cewa ba ta da adalci.

Siyasa rigar 'yanci: Diyar David Mark ta kunyata mahaifin ta a Benue

Siyasa rigar 'yanci: Diyar David Mark ta kunyata mahaifin ta a Benue
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An yi wata doka mai sarkakkiya ga matan aure a Saudiyya

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa diyar ta David Mark jim kadan bayan ta sauya shekar tare da dumbin magoya bayan ta da suka kai mutane dubu 15, ta kuma kai ziyarar ban girma ga dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar a zaben 2019.

A wani labarin kuma, alamu na nuna cewa kawunan jiga-jigan jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) sun rarraba musamman ma shugabannin ta da kuma gwamnonin jam'iyyar akan irin rawar da Bola Tinubu ke takawa a gangamin yakin neman sake zaben Shugaba Buhari.

Gwamnonin dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta ThisDay, suna nuna kishin su ne game da yadda jam'iyyar ta baiwa jigon ta Cif Bola Tinubu matsayi kusan dai dai da na shugaban kasa a wajen yakin neman zaben na sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel