Sabon rikici ya farraka kan jiga-jigan jam'iyyar APC a matakin kasa

Sabon rikici ya farraka kan jiga-jigan jam'iyyar APC a matakin kasa

Alamu na nuna cewa kawunan jiga-jigan jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) sun rarraba musamman ma shugabannin ta da kuma gwamnonin jam'iyyar akan irin rawar da Bola Tinubu ke takawa a gangamin yakin neman sake zaben Shugaba Buhari.

Gwamnonin dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta ThisDay, suna nuna kishin su ne game da yadda jam'iyyar ta baiwa jigon ta Cif Bola Tinubu matsayi kusan dai dai da na shugaban kasa a wajen yakin neman zaben na sa.

Sabon rikici ya farraka kan jiga-jigan jam'iyyar APC a matakin kasa

Sabon rikici ya farraka kan jiga-jigan jam'iyyar APC a matakin kasa
Source: UGC

KU KARANTA: An tafka kazamin fada tsakanin 'yan Boko Haram da sojin Najeriya

Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa gwamnonin suna nuna rashin jin dadin su akan yadda har wajen shugabancin shiyya-shiyya na kwamitin yakin neman zaben ba a saka su ba sai dai kawai aka saka wasu.

Gwamnonin kamar yadda muka samu, sun fara nuna shakkun su ne da irin karfin da ake baiwa Cif Tinubu din wanda suka ce ya wuce misali kuma hakan zai iya kawo masu matsala a nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel