Jirgin yakin soji ya lalata motocin yakin kungiyar ISWAP a Borno

Jirgin yakin soji ya lalata motocin yakin kungiyar ISWAP a Borno

Jirgin yakin rundunar sojin sama ya lalata motocin yakin kungiyar ISWAP a kusa da garin Damasak dake gabashin jihar Borno a wani hari da dakarun soji suka kai a wata maboyar 'yan kungiyar ta ISWAP.

Rundunar sojin ta kaddamar da hare-haren ne a jiya, Asabar, 5 ga wata, yayin bayar da agaji ta sararin samaniya ga dakarun soji dake yaki da 'yan kungiyar ISWAP bayan sun yi yunkurin kai masu hari a sansanin su.

Yayin ruwan wutar da jirgin yakin rundunar soji Mi-35 ya yi a kan 'yan ta'addar, an lalata motocinsu na yaki guda 3 yayin da aka kashe da dama da kuma raunata wasu, Kamar yadda sanarwar da Ibikunle Daramola, darektan hulda da jama'a na rundunar sojin sama.

Kalli faifan bidiyon a nan kasa:

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar a yau, Lahadi, ne dakarun sojin Najeriya dauke da bindigu suka yi dirar mikiya a ofishin jaridar Daily Trust dake garin Maiduguri, jihar Borno, tare da yin awon gaba da Editan jaridar, Uthman Abubakar, da wani ma'aikaci, Ibrahim Sawab.

Duk da rundunar sojin bata bayar da wani dalili na aikata hakan ba, jaridar ta ce faruwar hakan ba zai rasa nasaba da wani rahoto da ta buga a yau, Lahadi, ba a kan ofireshon din rundunar soji a yankin arewa maso gabas ba.

DUBA WANNAN: An kona gidaje da shaguna a sabon rikicin da ya barke a Ibadan

Daily Trust ta ce dakarun sojin sun rufe ofishin jaridar na Maiduguri bayan sun kama Editan da ma'aikacinsu.

Wani shaidar gani da ido ya ce dakarun sojin sun bukaci ganin Editan sashen harkokin siyasa na jaridar Daily Trust, Hamza Idris, wanda rubutunsa ya bayyana a labarin.

Har ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoton, rundunar soji bata fitar da wata sanarwa dangane da abinda ya faru ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel