Sojoji sun yi dirar mikiya ofishin Daily Trust a Maiduguri, sun awon gaba da Edita

Sojoji sun yi dirar mikiya ofishin Daily Trust a Maiduguri, sun awon gaba da Edita

A yau, Lahadi, ne dakarun sojin Najeriya dauke da bindigu suka yi dirar mikiya a ofishin jaridar Daily Trust dake garin Maiduguri, jihar Borno, tare da yin awon gaba da Editan jaridar, Uthman Abubakar, da wani ma'aikaci, Ibrahim Sawab.

Duk da rundunar sojin bata bayar da wani dalili na aikata hakan ba, jaridar ta ce faruwar hakan ba zai rasa nasaba da wani rahoto da ta buga a yau, Lahadi, ba a kan ofireshon din rundunar soji a yankin arewa maso gabas ba.

Daily Trust ta ce dakarun sojin sun rufe ofishin jaridar na Maiduguri bayan sun kama Editan da ma'aikacinsu.

Wani shaidar gani da ido ya ce dakarun sojin sun bukaci ganin Editan sashen harkokin siyasa na jaridar Daily Trust, Hamza Idris, wanda rubutunsa ya bayyana a labarin.

Sojoji sun yi dirar mikiya ofishin Daily Trust a Maiduguri, sun awon gaba da Edita

Dakarun Soji
Source: Depositphotos

Har ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoton, rundunar soji bata fitar da wata sanarwa dangane da abinda ya faru ba.

Sanann ne abu abu ne cewar rundunar soji ta sha gargadi da jan kunnen jaridu da ma jama'a a kan yada labaran da basu samu tushe daga rundunar ba.

DUBA WANNAN: Yiwa Buhari ihu a majalisa: Shehu Sani ya bayar da shaida a kan Dino Melaye

Ko a kwanakin baya bayan nan sai da rundunar ta fitar da kashedi ga masu yada labaran da basu inganta ba a dandalin sada zumunta, tare da yin gargadin cewar zata saka kafar wando daya da duk wanda ta samu na alakanta aiyukan rundunar da siyasa ko yada labarai marasa tushe domin tayar da hankalin jama'a.

Zamu kawo maku jawabin rundunar soji a kan wannan lamari da zarar sun fitar da sanarwa...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel