Harka ta lalace: Akwai yiwuwar Buhari ya kafa dokar ta baci jihar Zamfara

Harka ta lalace: Akwai yiwuwar Buhari ya kafa dokar ta baci jihar Zamfara

- Tsohon dan majalisar dattawan Najeriya daga jihar Zamfara, Sanata Dansadau yayi kira da gwamnatin tarayya ta nada shugaban soji a jihar har sai tsaro ya samu sannan

- Sanata Dansadau ya bayyana cewa wannan kiran ya zama wajibi ganin yadda kisa ya zama ruwan dare a jihar ta Zamfara

Dansadau dai wanda wakilci yankin zamfara na tsakiya ne a majalisar dattijai har sau biyu ya kalubalanci Gwamnan jihar Abdulaziz Yari da yin rikon sakainar kashi da yake yi ma jihar wanda kuma hakan yake kawo asarar rayuka.

Harka ta lalace: Akwai yiwuwar Buhari ya kafa dokar ta baci jihar Zamfara

Harka ta lalace: Akwai yiwuwar Buhari ya kafa dokar ta baci jihar Zamfara
Source: Facebook

KU KARANTA: Wuri 2 da Atiku ya zarta Buhari - Buba Galadima

Tsohon dan majalisar ya ce yanayin salon mulkin na gwamnan shine yake kara rura wutar rikice-rikicen jihar da take fama dasu da suka hada da satar shanu da kashe-kashe dama matsalar fyade.

Dansadau din ya soki gwamanan ida yace ya cika yawo a lokacin da kuma jihar tasa ke bukatar mulki na gari amma ba abunda yake yi sai yawo.

Dansadau din har ilayau yace tuni ya aike da takardar sa ta rokon a kafa ma jihar dokar ta baci zuwa ga shugaban kasa da kuma majalisar dattijai don in ba haka ba to rikicin zai iya karuwa yama fi na yanzu.

Dansadau ya kuma shaida ma manema labarai cewa: "A mazaba ta kawai kusan mutane 360 suka mutu sakamakon rikice-rikicen. Rayukan kuwa da aka rasa a fadin jihar basu ma misaltuwa. Wannan kuma duk saboda rashin iya mulki na gwamnan."

A tsawon lokaci akwai kyayyawar alaka tsakanin manoma da makiyaya amma cikin yan shekarun nan komai ya lalace sai fada kawai da kashe-kashe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel