Sauye-Sauye: An yi wata doka mai sarkakkiya kan matan aure a Saudiyya

Sauye-Sauye: An yi wata doka mai sarkakkiya kan matan aure a Saudiyya

Wata sabuwar dokar kasar Saudiyya mai cike da sarkakkiya za ta baiwa mata aure a kasar damar sani idan mazajensu sun sake su, sabanin yadda lamarin yake a da iyaye ko muharammin matar ne ke fara sani kafin daga bisani su sanar da ita.

Wannan sabuwar dokar dai kamar yadda muka samu, daga ranar Lahadi ne za ta fara aiki inda kotunan kasar za su bukaci mazan aure su aika wa matansu shaidar saki ta hanyar sakon wayar salula.

Sauye-Sauye: An yi wata doka mai sarkakkiya kan matan aure a Saudiyya

Sauye-Sauye: An yi wata doka mai sarkakkiya kan matan aure a Saudiyya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Yadda Aisha Buhari ta kunyata Ganduje a Kano

Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan mataki yana zuwa ne da ban mamaki a daidai lokacin da ake ta muhawara kan bai wa mata 'yancin tuka mota a kasar ta Saudiyya da ke bin tsarin addinin musulunci.

Haka zalika a yayin da wasu masu sharhi akan al'amurran yau da kullum ke ganin wannan matakin zai kara yawan mace-macen aure a kasar, ita kuwa hukumar kasar cewa tayi ta shigar da kara a kotunan kasar ne kan mazajen na sakin matan su ba tare da saninsu ba.

Don haka ana ganin yawanci mata ba su san takamaimai saki nawa mazan kan musu ba har sai idan auren ya kare baki daya sai iyaye su ce matar ta tattaro kayanta ta koma gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel