Tab-di-jan: Jihar Legas za ta kashe Naira Biliyan 850 a shekarar nan

Tab-di-jan: Jihar Legas za ta kashe Naira Biliyan 850 a shekarar nan

Gwamana Akinwumi Ambode ya makara wajen mikawa ‘yan majalisar dokokin jihar Legas kasafin kudin shekarar nan. A gobe ne aka tsammani gwamnan zai gabatar da kundin kasafin na shekarar bana.

Tab-di-jan: Jihar Legas za ta kashe Naira Biliyan 850 a shekarar nan

Ambode ya makara wajen gabatar da kasafin kudin shekarar nan
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa a gobe Litinin. 7 ga Watan Disamba ne gwamnan jihar Legas zai gabatar da kasafin da yayi na shekarar nan a gaban ‘yan majalisar jihar. Gwamnatin Legas za ta kashe sama da Naira Biliyan 800 a kasafin bana.

Akinwumi Ambode ya kasafta Naira Biliyan 852.317 a matsayin abin da jihar Legas za ta batar a 2019. Wannan ne dai karo na farko a cikin shekaru fiye da 10 da gwamnatin Legas ba gagara gabatar da kasafin ta kafin sabuwar shekara.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa abin da Legas za ta kashe a shekarar nan ya fi karfin abin da jihohi kusan 5 na Arewacin Najeriya su ka ware. Wadannan jihohin sun hada har da Kano, da Kaduna da kuma jihohin Jigawa, Gombe da kuma Katsina.

KU KARANTA: Ana jin ra'ayin jama'a a kan wanda zai lashe zaben gwamna a Kano

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya shirya kashe kusan Naira Biliyan 220 ne a bana, yayin da makwabcin sa, Nasir El-Rufai yayi kasafin Naira Biliyan 157. A jihar Katsina kuwa, an yi lissafin cewa a bana za a kashe Naira Biliyan 201.

Idan ba ku manta ba kuma, gwamnan jigawa watau Muhammad Badaru ya mikawa majalisar dokokin jihar kundin kasafin Naira Biliyan 157 ne wannan shekarar. Shi kuma Ibrahim Dankwambo ya na sa ran kashe Biliyan 118 a 2019 a jihar Gombe.

Idan aka hada dai za a fahimci cewa jihohin 5 za su kashe kusan daidai abin da Legas za ta kashe ita kadai ne a shekarar nan. A bara wancan ne ma jihar Legas tayi kasafin kudi na Naira Tiriliyan 1.04.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel