Yiwa Buhari ihu a majalisa: Shehu Sani ya bayar da shaida a kan Dino Melaye

Yiwa Buhari ihu a majalisa: Shehu Sani ya bayar da shaida a kan Dino Melaye

Sanata maj wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya tofa albarkacin bakinsa a kan rahotannin dake yawo na zargin Sanata Dino Melaye da yiwa Buhari ihu lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a gaban mambobin majalisar.

A ranar 19 ga watan Disamba ne wasu daga cikin mambobin majalisar tarayya suka yiwa Buhari ihu a lokacin da yake gabatar da jawabi a kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu yayin gabatar da kunshin kasafin kudin shekarar 2019.

Sanata Dino Melaye, mai wakiltar mazabar jihar Kogi ta yamma, ya musanta cewar yana daga cikin mambobin majalisar da suka yiwa Buhari ihu.

Tun bayan faruwar hakan, rahotanni a dandalin sada zumunta ke nuna cewar Melaye ne ya jagoranci yiwa Buhari ihu a zauren majalisar.

Yiwa Buhari ihu a majalisa: Shehu Sani ya bayar da shaida a kan Dino Melaye

Sanata Shehu Sani
Source: Twitter

Da yake kare kansa, Melaye ya ce bai yiwa Buhari ihu ba tare da bayyana cewar bai ma halarci zaman majalisa na ranar ba.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a kan wannan zargi da ake yiwa Melaye a shafinsa na Tuwita, Shehu Sani ya gaskata Sanata Melaye a kan cewar ba ya zauren majalisa a ranar da aka yiwa Buhari ihu.

"Sanata Dino Melaye bai halarci zaman majalisa ba a ranar da aka yiwa Buhari ihu," kamar yadda Shehu Sani ya rubuta a shafinsa na Tuwita a yau, Lahadi.

DUBA WANNAN: Zabe: Ganduje ya yiwa Aisha albishir mai dadi yayin kamfen din Buhari a Kano, hotuna

Tun kafin Shehu Sani ya bayar da wannan shaida, Legit.ng ta sanar da ku cewar sanatan da ke wakiltar yankin jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya bayyana cewa ba ya cikin ‘yan majalisar tarayyar da su ka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu kwanakin baya.

Sanata Dino Melaye ya karyata rade-radin da aka dade ana yadawa inda ya tabbatar da cewa ba ya cikin majalisar tarayya a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019 a karshen watan da ya gabata.

Fitaccen Sanatan yace don haka ba ya cikin wadanda su ka rika yi wa Buhari a lokacin da yake jawabi a gaban ‘yan majalisar kasar. Sanatan na jihar Kogi yayi wannan jawabi ne ta hannun wani hadimin sa, Gideon Ayodele.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel