Aisha Buhari ta kunyata Gwamna Ganduje wajen taron ta a Kano

Aisha Buhari ta kunyata Gwamna Ganduje wajen taron ta a Kano

Uwar gidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari a ranar Asabar din da ta gabata wajen taron da ta gudanar a jihar Kano ta kunyata Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje lokacin da ta tashi tayi tafiyar ta yana tsakar yin jawabin sa wajen taron.

Kamar dai yadda muka samu, uwar gidan shugaban kasar ta gudanar da wani taro ne ta kungiyar ta ta yakin neman sake zaben mijin ta karo na biyu da ta kunshi mata da matasa tare da kaddamar da shugabannin ta a jihar.

Aisha Buhari ta kunyata Gwamna Ganduje wajen taron ta a Kano

Aisha Buhari ta kunyata Gwamna Ganduje wajen taron ta a Kano
Source: Facebook

KU KARANTA: Hanya 2 da Atiku ya zarta Buhari - Buba Galadima

Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai a wajen taron bayan kammala jawabin ta a daidai lokacin da Gwamnan jihar ke nashi jawabin sai kawai aka ga ta tashi tayi tafiyar ta inda jim kadan kuma sauran mukarraban ta ma duk suka bi ta.

Kamar dai yadda jaridar DailyNigerian ta ruwaito, wannan ya sabawa al'ada kuma hakan bai rasa nasaba da irin yadda ba'a tsara jadawalin taron ba yadda ya kamata wanda hakan bai yi wa uwargidan shugaban kasar dadi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel