Hanyoyi 2 da Atiku Abubakar ya zarta Shugaba Buhari a ra'ayin Buba Galadima

Hanyoyi 2 da Atiku Abubakar ya zarta Shugaba Buhari a ra'ayin Buba Galadima

Fitaccen dan siyasar nan kuma dan gwagwarmaya sannan kuma tsohon na hannun damar shugaba Buhari a siyasance a da watau Injiniya Buba Galadima ya bayyana hanyoyi biyu da dan takarar shugabancin kasa a PDP, Atiku Abubabar ya zarta Shugaba Buhari.

Buba Galadima ya bayyana hakan ne a cikin wata fira da yayi da gidan Jaridar Blueprint a karshen makon nan yayin da yake ansa tambayar da aka yi masa game da cewa ko 'yan Najeriya na da zabin da yafi Buhari a zaben 2019.

Hanyoyi 2 da Atiku Abubakar ya zarta Shugaba Buhari a ra'ayin Buba Galadima

Hanyoyi 2 da Atiku Abubakar ya zarta Shugaba Buhari a ra'ayin Buba Galadima
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Kwastam sun cafke motar Dangote makare da haramtattun kayayyaki

Legit.ng Hausa ta samu cewa Buba Galadima ya bayyana cewa tabbas Atiku yafi Buhari a wurare akalla 2 kuma shi ne ya kamata 'yan kasar su zaba idan lokaci yayi domin maido da kasar a turbar da ta dace da ita.

Da yake karin haske a maganar ta sa, Buba Galadima yace na farko dai Atiku ya fi Shugaba Buhari kwarewa a fannin mulki da kasuwanci wanda kuma mai irin hakan ne kadai kasar ke buka yanzu ba ba tsohon soja ba.

Haka nan ya kara da cewa Atiku mutum ne mai tausayi da ba zai taba bari a rika kashe jama'a ba a garuruwa irin Borno da Zamfara ba tare da ya dauki mataki ba kamar yadda shi shugaba Buhari yayi kunnen uwar shegu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel