Da dumin sa: An yi musayar wuta tsakanin sojin Najeriya da 'yan ta'addan Boko Haram

Da dumin sa: An yi musayar wuta tsakanin sojin Najeriya da 'yan ta'addan Boko Haram

- An gwabza kazamin fada tsakanin sojin Najeriya da 'yan ta'addan Boko Haram

- An yi musayar wuta tsakanin sojin Najeriya da 'yan ta'addan Boko Haram

Dakarun sojojin Najeriya a ranar Asabar din da ta gabata sun yi musayar wuta tsakanin su da 'yan ta'addan da aka kyautata zaton 'yan Boko Haram be a lokacin da suke kokarin kwace garin Damasaka dake a jihar Borno ta Arewa maso gabashin Najeriya.

Da dumin sa: An yi musayar wuta tsakanin sojin Najeriya da 'yan ta'addan Boko Haram

Da dumin sa: An yi musayar wuta tsakanin sojin Najeriya da 'yan ta'addan Boko Haram
Source: Twitter

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun yi luguden wuta kan 'yan bindiga a Zamfara

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta Daily Trust, 'yan ta'addan da ake kyautata zaton yan bangaren Mus'ab Albarnawi ne dake da alaka da kungiyar ta'addancin nan ta IS dake da hedikwatar ta a yankin gabas ta tsakiya.

Legit.ng Hausa ta samu daga wani da lamarin ya auku akan idon sa cewa dakarun sojin Najeriya sun yi wa maharan kofar raggo inda suka zagaye su yayin da suke kokarin shiga garin na Damasak sannan suka far masu tare da kashe da dama daga cikin su.

Mai karatu dai zai iya cewa a 'yan kwanakin baya dai 'yan ta'addan Boko Haram sun ci garuruwa da dama da yaki a jihar ta Borno ciki hadda Baga da aka ruwaito cewa har tutar su ma suka kafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel